Main menu

Pages

HANYOYI UKU DA ZA ABI WAJEN GYARAN JIKI DA MATAKAN DA ZAKI BI

 



Matakangyaran jiki da Kuma yadda za a gyara jiki da Dilka, Alkama da Kuma Khalda(Oats)


Yadda Ake Gyaran Jiki Yai Laushi Kuma Yai Kyau: Gyaran jiki yana taimakawa Namiji ko Mace ta daɗe tana more jikinta. Fatar mutum ta zama lafiyayya, kuma abin sha’awa. Shi ne za ka ga mace komai yawan yawan haihuwarta, Tana da kyakkyawan jiki.




Gyaran jiki ya samo asali ne daga wajen Larabawa. Sai Barebari wato daga Maiduguri, a nan Ƙasar NIjeriya. Haka ma Turawa sun yi mayuka kala-kala domin gyara fata.



Sai dai duk Sanda mutum yake so zai dinga gyara jiki. To ya zama tilas ya kula da mafi muhimmanci, wato ya bi matakai na gyara jiki.



Matakan Gyaran Jiki

1 – Cin lafiyyen abinci.

2 – Yawan Shan ruwa .

3 – Yawan Cin ‘ya’yan itatuwa.

4 – Atisaye ( motsa jiki) .

5 – Amfani da kayan gyaran jiki ( Dilka).




Gyaran Jiki na Dilka:

Za a zuba Dilka a cikin mazubi. Sai a zuba masa ruwan zafi. Bayan jimawa sai a zuba kurkum, da man zaitun, da ƙwai .

Sai a ƙara ruwa ɗan daidai. A shafe dukkan jiki har fuska. Idan ya bushe sai a murje jiki da shi.




Gyaran Jikin Alkama

Za a nika Alkama ne, a tankaɗe ta, tai lukwui. Sai a soya ta kamar yadda ake idan za a yi kunun alkama.

Za a zuba wa soyayyiyar alkama yis. A zuba ruwa a kwaɓa ta. A shafe duk jiki da ita. Bayan ɗan lokaci, sai a dinga murje jiki ko’ina.




Gyaran jiki da Khalda( Oats):

Za a zuba wa khalda (Oats) madara. Sai kuma a matsa lemon tsami kadan. A juya shi a kwaɓa sosai. Sai a shafa amma shi duk jiki. Bayan ɗan lokaci sai a murje duk jiki.


A ƙarshe, lallai akwai buƙatar mu dinga waiwayar gyaran jikinmu, duk sati in da hali. Ko kuma duk Wata. Ya danganta da yadda ake da hali, lokaci da himma.

Comments