Main menu

Pages

ABUBUWAN GUDA BIYAR DAKE DAKUSHE NI'IMAR MACE




Abubuwan dake Dakushe Ni'imar Mace har ma ta kasa amsa sunanta na matsayin Mace.


Akwai abubuwa masu yawan gaske da suke haddasa rashin gamsar da maigida wata macen ma bata san cewa bata gamsar da maigidanta ba, sai dai kawai taga yana wulakantata yana nuna mata"kiyayya don duk matar da bata gamsar da mijinta to dole ne ya gallaza mata, dole ne yayi mata ukuba, dole ne ya wulakantata ,duk irin dimbin soyayyar da yake yi miki kuwa ba zata yi tasiri ba, don haka sai ki gyara, kaima idan ka gani ka fadawa matar ka domin ta gyara.




 1 Tafiya babu Takalmi: Yawo a cikin gida babu takalmi, ba karamin jefa mace yake cikin hadari ba, don yana rage mata ni'ima sosai ko da kuwa kina da wadatacciyar ni'ima rashin sanya takalmi zai iya cutar da mijinki ayi hattara!




 2 Samuwar Faso ko Kaushi: Shima yana haddasawa mace rashin gamsar da maigidanta don haka a kiyaye!




 3 Jinkirya yin wankan Haidah: Don a yadda akeso idan mace ta gama al'ada tana gamawa ta sami auduga tasa turaren miski tasa a farjinta zuwa wani dan lokaci ta cire tayi wanka.



 4 Rashin cin abinci Mai Gina jiki: shima yana haddasawa mace rashin ni'ima.



 5 Amfani da magunguna Mata barkatai

 Shima a karshe yana haddasawa mace bushewa, saboda yana matso miki ruwan jiki ne da tsiya, yau da gobe kuma zai kare shikenan kin shiga matsala idan baki cin abinda zai kawo ruwan, ayi hattara! Bako wanne magani zaki dauka kiyi amfani dashi ba ki tabbatar da ingancinsa kuma kin tabbata babu sihiri a ciki.


Comments