Main menu

Pages

ABUBUWA GUDA BAKWAI (7) DAKE JANYO NANKARWA A JIKI,




Abubuwan dake janyo nankarwar jiki, da yadda za a magancesu su bace bat

Nankarwa wasu  layukane marasa kyau gani da suke fitowa a jikin dan adam mace ko na miji wurare kamar su;-

Ciki daga kasa ko, mara ko, Saman mama ko, duwawu ko, Cinya dadai sauran sassan jiki.


      

   Abubuwan da suke kawo Nankarwa 

1. Daukan ciki zuwa haihuwa

2. yin kiba tashi guda 

3. Yin rama tashi guda

4. gado daga mahaifiya

5. damuwa mai yawa da makamantar su.

6. Jinya na tsawon lokaci

7. Shafa mayukan sake fata daga baka zuwa fara tas.

 




        Yanda za a hada maganin

Asamu man zaitun da man ridi da man habbatus sauda da man kadanya, duk yawansu ya zama daya sai ahadasu waje guda agarwaya.



Arika shafawa bayan anyi wanka safe da dare, har awarke.

Comments