Main menu

Pages

MATAKAI GUDA 7 DA MACEN DAKE SON SAMUN CIKI ZATA BI

 Wasu matakai har guda Bakwai da Macen dake son samun juna biyu zata bi idan Allah Ya so.


Shawara mafi muhimmanci ga mace da ke son daukar ciki ko samun juna-biyu ita ce sanin yanayin jikinta, musamman lokacin zuwan jinin al'adarta, a cewar Dakta Sajeeda Ibrahim, ƙwararriyar likitar mata a Asibitin Koyarwa na birnin Tarayyar Najeriya, Abuja.
"Yana da muhimmanci ta san yanayin zuwa da ɗaukewar jininta na haila saboda tsara ko sanin lokutan da idan ta yi jima'i za ta dauki ciki," a cewar Dakta Sajeeda.

BBC ta tattauna da Dakta Sajeeda da kuma Dakta Tanko Zakari, kwararre kan lafiyar mata a Asibitin Mallam Aminu Kano, kan matakai bakwai da za su taimaka wa mace wajen ɗaukar ciki.
1. Bincike domin sanin yanayin lafiyar jikinki

Kafin ki soma kokarin ɗaukar ciki, ki soma duba lafiyarki. Ki tambayi likitarki domin samun bayanai kan magunguna da ke taimakawa mace wajen ɗaukar ciki - masu dauke da sinadarin folic asid da ke taimakawa da kuma bayar da kariya kan wasu matsalolin haihuwa da suka hada da haihuwar jarirai masu nakasa.Sinadarin folic asid na aiki sosai a kwanakin farko na ɗaukar ciki, shi ya sa yake da muhimmanci ki tabbata kina shan sa sosai tun kafin ki yi ciki.
Ki tabbatar kina bin wannan tsari kafin kokarin ɗaukar ciki, a cewar Dakta Sajeeda. "Idan kina da matsala da lalura dole ki nemi magani da daidaita kanki kafin ki samu ciki ba tare da matsala ba."
2. Sanin lokutan haila:

Me kika sani game da lokacin zuwa da ɗaukewar hailarki? Fahimtar hakan zai taimaka miki wajen sanin lokacin da ya fi dacewa na daukar ciki a gare ki a cewar, Sajeeda.Lokacin da mahaifar mace take fitar da kwayaye shi ne mafi dacewa wajen daukar juna-biyu a gare ta.

"Wannan shi ne lokacin da ake son mace ta nuna nacewa wajen jima'i a kai-a kai," a cewar masana. Sai dai Kuma Allah Shine Mai yi, yadda duk Ya hukunta hakan ne zai kasance.
Hakan na taimakawa wajen gane alamomin fitar kwai, da sauye-sauye da mace ke ji a jikinta da fitar ruwa daga farjinta.

Ruwan na kasancewa fari da ɗan kauri da yauƙi wanda ke isar da sakon cewa shi ne lokacin iya samun juna-biyu. Wasu mata kuma kan yi fama da ciwon mara.Sannan akwai abin da ake amfani da shi wajen gwada ko mace ta soma fitar da ƙwai wanda shi ma yana taimakawa wajen ankarar da cewa tana cikin lokacin iya ɗaukar ciki, a cewar Dakta Sajeeda.
Ba wai kawai za su tabbatar miki da cewa lokacinki na fitar da kwai ya zagayo ba ne, "idan kina jima'i akai - akai, wannan na sanar da ke lokacin da ya kamata ki sake bayar da karfi domin daukar ciki," a cewarta.

Ga yadda lissafin yake: Ranar farko ta ganin jinin halarki, da ita za ki soma lissafi.


"Ki soma gwaji daga rana ta tara ki kuma ci gaba da hakan har sai gwajin ya tabbatar miki da lissafin.Mata da ke ganin haila bayan duk kwanaki 28 na iya soma fitar da kwai a rana ta 14.


Sai dai galibin mata yanayin hailarsu na da tsayi wasu kuma gajeren lokaci suke dauka, don haka dole ki natsu wajen tantace lissafinki.
Mece ce makomar masu amfani da magungunan takaita haihuwa? Dole sai kin dan jinkirta kafin ki samu juna-biyu? Likitoci dai na cewa ba lallai ba ne."A shekarun baya, wasu bayanai na cewa sai ka ɗan jira na wani ɗan lokaci bayan ka dakatar da shan kwayoyin hana daukar ciki kafin ka shiga fafutikar neman ciki, sai dai wannan karatun a yanzu ya sauya.


Kina iya kokarin ganin kin dauki ciki da zarar kin daina shan magungunan takaita haihuwa," a cewar Dakta Tanko Zakari, kwararren likitan mata a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano.
Dakta Tanko ya ce abin da mace ya kamata ta sa a zuciyarta shi ne tana iya daukar ciki kafin zuwan haila, don haka lissafin lokacin fitar kwan haihuwa na iya kasancewa mai wahala, kuma kina iya shan wahala wajen iya gano lokaci ko ranakun da za ki soma fitar da kwan haihuwa.

Bisa wannan dalili, "wasu kan jira har sai zagayowar jinin haila," a cewarsa.
3. Salon kwanciya mafi kyau:

Tatsuniyar salon kwanciya mafi dacewa saboda daukar ciki cikin gaggawa, wannan kusan labari ne ko shaci-faɗin mutane.


Gaba daya dai Wannan matakan ana ganin zasu taiamaka ne idan Allah Ya so Ya Kuma qaddara samuwar cikin. Allah Ya sa a dace.

Comments