Main menu

Pages

AMFANIN YAWAITA SHAN RAKE GA MAI CIKI DA YARON DAKE CIKI, DA SAURAN FA'IDODINSA

 Fa'idodin yawaita Shan Rake ga Mai ciki da inganta Lafiyar yaro, da Kuma Kara Ni'ima da sauran fa'idodi inji wata likita.


Wata kwararriyar likitan bangaren abinci a Babban Asibitin Agege dake jihar Legas, Misi Olufunmilola Adewumi ta shawarci masu bukatar karin ni'ima da karfin sha'awa da su dage da shan rake.
A zantawarta da Kamfanin Dillancin Labarai  na Najeriya (NAN) ranar Litinin, kwararriyar likitar ta ce shan raken zai iya taimakawa mata masu matsalar ciwon mara samun sauki yayin daukar ciki da kuma samun saukin haihuwa.
 A cewarta, rake na dauke da isassun sinadaran kara ni'ima kamar nutrient da vitamin C da vitamin B2 da magnesium da iron da potassium da kuma phosphorus.
Ta ce, “Rake na dauke da sinadaran dake kare jariri a cikin mahaifiyarsa daga cututtuka da dama.“Tana kuma taka muhimmiyar rawa wajen kara karfin gaba da kuma kara ruwan maniyyi.


“Tana taimakawa wajen rage matsalar kankancewar gaba,” inji Olufunmilola.
Likitar ta kuma ce baya ga wadannan fa'idojin, shan rake a kai a kai na taimakawa wajen takaita tasirin cututtukan da ake dauka ta hanyar jima'i.
“Ta kan rage cututtukan dake da alaka da mafitsara da koda da kuma duwatsun ciki, musamman in aka hadata da lemon tsami da ruwan kwakwa,’’ inji ta.Daga nan sai ta shawarci a rika shan akalla mililita 400 na raken a kullum 

domin samun cikakkiyar fa'idarta.


Sai dai ta yi gargadi kan cewa shan raken fiye da kima na iya rikita ciki, ya kawo rama, ciwon kai da kuma yawan jin bacci.

Comments