Hadin maganin ciwon Mara kowane irin ne ga Maza da Mata.
"Nasiha ga mai hada maganin, kafin ka hada ka sani cewar shi magani ana shansa ne a matsayin sila hakikanin waraka tana hannun Allah ka gwada maganin ka barwa Allah Ikon Sa".
"Wannan Maganin Ka Daure Ka Hadashi Ka Jarraba Insha Allah za'a sauki' Kuma Wannan Magani Na Miji Ko Mace Kowa Zai Iya Amfani Dashi"
Mata masu gama da zafin mara a yayin da Al'ada tazo musu zasu iya Jarrabawa kuma da yardar Allah za'a dace kuma ayi Hamdala'
Abubuwan da za a hada sune kamar haka:
1- Tsamiya guda biyu' ma'ana tsamiya sili biyu
2- Garin habbatus-Sauda Cokali daya.
3 - Ruwa kofin shayi babba guda biyuZ
4 - Zuma pure mai kyau wadda babu gauraye a ciki
Idan komai ya samu cikin abinda muka lissafa, sai a hada maganin kamar haka;
Za a samu ruwan kofin shayi biyu a dora shi akan murhu sai a saka silin tsamiya guda biyu a zuba garin Habbatus-sauda Cokali daya, sai a tafasa su' idan sun tafasa sai a samo zuma kamar Cokali biyu ko Uku sai a raba Ruwan Biyu' zai zama kofi daya kenan' Sai a zuba zumar cokali biyu ko Uku A shanye
A ajiye Daya Kofin' idan yamma tayi' Sai a Kara Tafasashi' a zuba zumar Cokali biyu ko uku' A Samu Kamar Wata Huda Anayi Insha Allah Ciwon Mara Ko Wanne Irine za'a Rabu dashi''
Comments
Post a Comment