Hanyoyi Guda Goma ga wanda Ya tsinta Kansa a cikin kunci da damuwa zai bi don warwarewar matsalar da.
(Sheikh Muhammad Rabi’u Rijiyar Lemo) .
Babu ko shakka kowa a yau ya san al’ummar musulmi a Duniya suna cikin halin kunci da damuwa, don haka wajibi ne malamai da daliban ilimi su ci gaba da haskawa al’umma hanyoyin da ya kamata su bi don samun mafita daga wannan bala’i da musifa.
Ga wasu hanyoyi goma da zamu runguma da izinin Allah, Allah zai yaye mana wadannan musifu: .
1. Kyautata imani da Allah da nisantar abin da yake tauye imani : Allah ya yi alkawarin taimakon bayinsa muminai, da basu nasara akan abokan gabarsu. Don haka matukar akwai imani da Allah a zukatan bayi to Allah ba zai tozarta su ba. .
2. Tuba da Istigfari da Komawa zuwa ga Allah. .
3. Yawaita ayyuka na kwarai, saboda ayyukan kwarai sukan kawo wa zuciya nutsuwa, kamar yadda munanan ayyuka sukan kawowa zuciya bakin ciki da damuwa da kunci.
4. Yawaita Sadaka : musammam ma a boye ba tare da an sani ba, ya tabbata a hadisi Manzon Allah S.A.W ya ce “Aikata kyawawan ayyuka suna kawar da munanan abubuwa, sadakar boye tana kawar da fushin Ubangiji, sada zumunci yana kara tsawon rayuwa, dukkan aikin alheri sadaka ne, masu aikin alheri a duniya, su ne ma’abota alheri a lahira, masu munanan ayyuka a duniya, su ne masu ma’abota mummuna a lahira, farkon wadanda za su shiga Aljannah su ne masu aikata kyawawan ayyuka”. (Dabaran i ne ya rawaito shi.)
5. Addu’a : ba don addu’a ba da mutane da yawa sun halaka. Allah madaukakin Sarki yana jarrabar bayinSa da bala’i don su koma gare shi, su kaskantar da kai da addu’a, idan suka koma zuwa gare shi, suka kasakantar da kai sai ya yaye musu. .
6. Umarni da kyakkyawan aiki da hana mummuna : Allah ba zai halaka al’umma ba, matukar akwai masu umarni da kyakkyawan aiki da hana mummuna.
7. Nisantar Zalunci Allah ya halakar da al’ummu da yawa saboda zalunci. Mafi girman zalunci shi ne shirka da kafirci, sai zaluntar bayin Allah a cikin dukiyarsu da mutuncinsu da jininsu, mu nisanci zalunci mu zauna lafiya. .
8. Zikiri wato ambaton Allah, da baki da zuciya da gabbai. Da ambaton Allah ne zukata suke nutsuwa. .
9. Neman ilimin addinin musulunci : Al’umma tana tsira daga halaka idan akwai malamai a cikinta, wadanda za su kama hannunta daga duhu zuwa haske, daga shirka zuwa tauhidi, daga bidi’a zuwa sunnah. Duk al’ummar da ta bar ilimin addini ta shagala da na rayuwa to tana tare da kunci da bakin ciki da rashin kwanciyar hankali. .
10. Hakuri da Juriya : Hakuri wajen bin Allah, hakuri wajen barin sabon Allah, hakuri akan abin da Allah Ya kaddara, samun nasara yana tare da hakuri. . Allah ka kara mana hakuri wajen yi maka da’a, da barin abin da ka hana, ka yafe mana kurakuranmu.
Comments
Post a Comment