Abubuwan da suke Haifar da Kumburin Mahaifa Mai sanya zubar jini (Endometriosis) da Yanda za a mangance Matsalar.
Endometritis kumburin bangon mahaifa ne (endometrium) wanda yake haddasa zubar jini daga gaban Mace. Zai iya kasancewa mai tsanani amma baya daukar dogon lokaci (a cute). Hakanan zai iya zamowa mai tsanani kuma mai daukar dogon lokaci (chronic).
Mafi yawanci kwayoyin cutar bacteria ne suke kawo shi, musamman wadanda suke kama al'aurar Mace bayan ta haihu, ko kuma a lokacin da ake yi mata aikin tiyata a mahaifa ko mara.
Bincike ya tabbatar da cewa manyan dalilai masu kawo endometritis sune:
1. Haihuwa (childbirth): Idan kwayoyin cutar bacteria suka shiga cikin mahaifa a lokacin da Mace take yin nakudar haihuwa, to, zasu iya haddasa mata matsalar endometritis, musamman idan tayi doguwar nakuda (prolonged labour), ko yagewar jakar ruwan mahaifa (amniotic sac rapture), ko yawan duba mata budewar farjinta (multiple vaginal examination - VE).
2. Aikin tiyatar cire jariri (caesarian section - CS): matan da aka yiwa tiyatar CS sunfi kowa hatsarin kamuwa da endometritis, duk da kasancewar kayan aikin da kuma dakin tiyatar masu matukar tsabta ne. Hakan yana da nasaba da tsananin yawa ko kankantar bacteria din ne.
3. Ayyukan tiyatar da suka shafi farji da marar Mace (gynaecological procedures): wadannan sun kunshi wankin ciki (dilation and evacuation), aikin duba mahaifa (hysteroscopy), daukar wani abu daga cikin mahaifa domin yin awon wata cuta (endometrial biopsy). Kwayoyin cutar bacteria zasu iya shigar mahaifa a lokacin wadannan ayyukan.
4. Cututtukan da ake dauka a wajen jima'i (sexually transmitted diseases - STDs): wadannan sun kunshi chlamydia, gonorrhea, staphylococcus, da sauransu. Duk suna iya haifar da endometritis idan suka shiga mahaifa.
Alamomin kamuwa da cutar (Symptoms)
Alamun endometritis sune:
1. Zubar ruwan da Mace bata saba gani ba daga gabanta (abnormal vaginal discharge): ruwan zai iya kasancewa mai wari ko karni, sa'annan mai launin ruwan kwai (yellowish) ko ruwan ganye (greenish).
2. Ciwon mara (pelvic pain): Mace mai matsalar endometritis zata rika fuskantar ciwon mara mai tsanani, kodai mai dadewa bai bari ba ko kuma mai zuwa ya tafi.
3. Zazzabi da jin sanyi (fever and chills): shima zai iya zamowa mai tsanani, sa'annan mai zuwa ya tafi ko mai dadewa.
4. Jin zafin fitsari ko yawan yin fitsari (dysuria or polyuria): shima zai iya zama mai zuwa ya tafi ko mai dadewa.
5. Zubar jini mai yawa lokacin al'ada ko rashin tsayayyar al'ada (heavy or irregular menstrual bleeding): shima zai iya zama mai zuwa ya tafi ko kuma mai dadewa.
Matsalar da yake haifarwa Mace (Effects)
Idan ba'a magance endometritis ba, zai iya haifar da:
1. Rashin haihuwa (infertility): hakan zai faru ne sakamakon raunana da kuma lalata halittun mara na haihuwa.
2. Taruwar ruwan gunya a cikin mara (pelvic absess): zai iya haifar da gyambo mai tara ruwan gunya a cikin mahaifa.
3. Kumburin dukkan jiki (sepsis): hakan zai iya faruwa ne sakamakon yaduwar kwayoyin cuta a dukkan sassan jiki ta hanyar jijiyoyin jini.
Hanyoyin da za a yi rigakafi (Prevention)
Za'a iya rigakafin kamuwa da endometritis ta hanyar:
1. Inganta tsabta a lokacin karbar haihuwa, da lokacin yin tiyatar mahaifa a marar Mace, domin kaucewa yaduwar kwayoyin cuta.
2. Tsabtace kayan ayyukan tiyata yadda ya kamata.
3. Tabbatar da cewa ma'aurata basu dauke da cututtukan da ake dauka a wajen jima'i.
Yanda za a magance (Treatment)
Hanyar magance endometritis ita ce zuwa asibiti domin likita ya yi aune-aune kuma ya dora Mace akan maganin antibiotics da ya dace. Idan abin ya ta'azzara, to, sai an kwantar da ita.
WalLahu A'lam.
Comments
Post a Comment