Main menu

Pages

ABUBUWAN DA SUKE HADDASA DAUKEWAR NI'IMA GA MACE

 


Abubuwan dake haddasa daukewar ni'ima ga Mace.

Sau dayawa mata ke damuwa akan daukewar ni'ima ko bushewar gaba har sai sunyi amfani da lubricants.



Amma menene alamomin bushewar gaba?

1. Yawan jin kaikayi ko zafi a gaban mace 

2. Jin ciwo yayin saduwa.

3. Shan wahala kafin namiji yasami damar shigan macce

4. Ganin jini lokacin saduwa

5. Jin zafi lokacin saduwa

6. Rashin jin sha'awar namiji

7. Yawan zuwan infection akai akai babu dalili, musamman masu juna biyu




Ga wasu daga cikin abubuwan dake kawo bushewar gaba da bayanansu.

1️⃣ Infections: Duk lokacin da mace ke fama da infection, kowane kalan infection ne (bacterial, fungal, viral ko protozoan vaginal infection) wadannan kwayoyin cutar zasu hana gaban mace yin aikin shi yanda yakamata, tayanda ruwan dake fitowa a gaban mace su daina zuwa saidai wasu ruwan masu wari ko karni na infection ko jini



2️⃣ Tsufa ko tara shekaru: duk lokacin da shekarun macce suka haura 35, toh jikin ta zaya rage producing oestrogen hormone (shi wannan oestrogen shikesa gaban mace ya rika sako wadannan ruwan na niima, sannan shike kula da duk wani abu da ya shafi saduwa, jindadi, juna biyu da sauran su)


Akwai wasu dalilai dake sa Oestrogen hormone ya rage a cikin jini ko mace bata tara shekaru ba 15 zuwa 30 kamar haka.

1- Yawan motsa jiki da aikin kiza kiza kamar namiji

2. Tunani da damuwa

3. Shayarwa idan macce ta haihu

4. Shan sigari

5. Shan giya da magungunan maye

6. Rashin lafiya kamar hawan jini ko ciwon sugar

7. Magungunan family planning

8. Idan akayi macce theatre ga ovaries misali (PCOS)

9. Duk wadansu magungunan da zasu iya alaka da hormones kamar su DEXAMETHASONE da sauran su.

Duk wadannan dalilan suna kawo karancin OESTROGEN a jiki ta har yakai gaban macce ya bushe

Comments