Main menu

Pages

HADIN MATAN AURE, GA MATAR DAKE FAMA DA RASHIN SHA'AWA

 Ingantaccen Hadi ga Matar Auren dake fama da daukewar Sha'awan.

Wasu matan kan yi kukan rashin sha'awar jima'i. Akan samu mata da ke fama da wannan matsala da har ta kai ta kawo, a dole ta ke saduwa da mijinta, amma ba wai don ta na da sha'awar jima'in ba. Da iznin Allah idan ta yi wannan hadin ta yi amfani da shi za ta kasance mai sha'awar jima'i.
Kayan Hadin Da Ake Bukata:

a. Sassaken Baure, babban cokali 5

b. Kanumfari, babban cokali 3

c. Zuma, babban cokali 2

d. LiptonYadda za ta hada, za ta daka sassaken bauren bayan ta bar shi ya bushe don ta samu garinsa. Sai ta daka kanumfari, shi ma don ta samu garinsa. Za ta gauraya garin kanumfarinta babban cokali 3 da garin bauren babban cokali 5, bayan ta tabbatar sun gaurayu sai ta zuba zuma babban cokali 2 ta cakuda su, su cakudu sosai. Za ta debi karamin cokali daya na wannan hadi ta zuba cikin ruwan lipton ta sha sau biyu a rana.

Comments