Main menu

Pages

YANDA ZAKIYI AMFANI DA GISHIRI BAYA GA SANYAWA A CIKIN GIRKI

 



Amfanin Gishiri, wajen yin dabarun yin wasu abubuwan a cikin gida.

Gishiri yana da amfani da yawa bayan zubawa a cikin abinci, mutane da yawa sun zata amfanin gishiri shi ne kawai a zuba a cikin miya, amma ina, amfaninsa ya fi ga haka. 




Amfanin Gishiri kwararru a fannin kiwon lafiya sun tabbatar cewa baicin abin da muka sani na al’ada, wato amfanin Gishiri cikin miya, hakikatan sun tabbatar cewa Gishiri dai yana da dimbin sirruka da amfani ga dan adam.



 

 1. Na farko, kowa ya san cewa idan Kyandir ya diga a waje, tilas zai manne da wajen, har sai an kankare shi da karfin tuwo, amma muddin ki ka jika Kyandir din cikin ruwan Gishiri, na tsawon awa biyu ko uku, to da zaran kin kunna shi, yana ci, ko da zai diga a waje, ba zai kama ba. Za ki sha mamaki, domin da kin dan murje shi, zai fita, tamkar Kyandir bai taba diga wajen ba. 




2. Ina mata masu amfani da risho ko abin gashi irin na lantarki ko wanda ake amfani da Gas?

 Mafi yawan lokaci idan kina girki za ki ga ruwan girkin ko man gyada da ki ka yi suya da shi, ko dai wani abu da ki ka dafa a kan risho ya bata shi sosai, kafin kuma ki gama girkin ya bushe, don haka da rishonki ya fara baci sai ki barbada gishiri a wajen, da kin gama girki idan ya huce kina saka soso za ki ga ya fita.

 Haka ma za ki yi wa dukkanin ababen girkin ki. 




3. Idan kina tantaman kwai ko ya lalace ko yana da kyau, sai ki zuba gishiri karamin cokali biyu a cikin ruwa, ki kada, ki zuba kwan a ciki, idan yana da kyau za ki ga kwan ya yiwo sama yana yawo, idan kuma ya lalace ne kuma za ki ga ya yi kasa, sabanin abin da aka saba gani. 




4. Sosan wanke-wanke idan ba a tsaftace, shi sai ya zama waje ne da kwayoyin cuta suke dabdalarsu a ciki, don haka duk lokacin da ki ka gama wanke-wanke ki wanke sosan sosai, sai ki jika shi a cikin ruwan gishiri na awa daya ko biyu, kuma da zarar kin ga ya fara lalacewa ki yar da shi ki sayi wani, ba wani tsada ne da shi ba. 




5. Idan kin sayi tsintsiya kuma kina so ta dade miki, idan kin sayo tsintsiya kafin ki fara amfani da ita sai ki jika da ruwan Gishiri.

Comments