Main menu

Pages

YANDA ZA A MAGANCE MATSALAR FURFURA DAKE FITOWA AKAN YARA KO MATASA
Matsalar dake haifar da fitowar Furfura ga wadanda ba tsoffi ba, da yadda za a Magance Matsalar.

A shekarun da suka gabata tsofaffi ne ake danganta su da farin gashi a ka, wato Furfura, amma yanzu abin ya canza, sai kaga har jariri ma akan haife shi da farin gashi a ka.
Irin wannan ce ta sa wasu masana suka gudabar da bincike inda suka musanta cewa ba duka Furfura bace take zama halitta daga Allah, akwai abubuwan da ke kawo su.Kwararrun sun bayyana cewa fitowar furfura a jiki ya rabu kashi biyu ne; akwai wanda nasu halittace daga Allah sannan da wanda yake fitowa saboda rashin garkuwar jiki wadda take da karfi.
Likitocin sun bayyana cewa an halicci jikin mutum da garkuwa da take taimakawa wurin kare shi daga kamuwa da cututtuka.


‘‘Furfura kan fito a jikin mutum musamman ma karamin yaro idan garkuwar jiki nasa bata da karfin kare shi daga kamuwa da cututtuka.”
Domin kaucewawa irin hakan ne kwararrun suka bayyana wasu hanyoyin da za su taimaka wa mutum guje wa samun garkuwar jiki mara sa karfi.
Hanyoyin sun hada da:

1.Yawaita cin abincin da yake dauke da sinadarin dake karfafa garkuwar jiki kamar su ganye, kayan lambu, madara, kifi, da sauransu.


2. Samun isasshen hutu musamman ga wadanda suke ganin cewa hutawa lalaci ne.


3. Rage damuwa, domin yawan damuwa na kawo tsufa da wuri.

A rika motsa jiki, domin yana taimakawa wurin bunkasa garkuwar jiki.


4. A rage shan  giya, yawan cin maiko, kanzon tukunya da sauran makamantansu.


5. A kuma rika tsaftace jiki.

Comments