Yadda Ake Hadin dahuwar Kifi Domin Saukar Ni'ima cikin sauri.
Kasancewar Ki mace yar'lele kuma kullum amarya wacce maigida yake mararinki abune Mai sauki a gurin ba boka ba mallam to zamo mai gyara jikinki.
Kayan da Zaki bukata
- Kifi (sadin)
- Man gyada
- Alayyahu
- Albasa
- Kayan dandano na kamshi
Ki sami kifi Ki cire kayar Ki wankeshi Ki sami tukunya mai kyau Ki sulala kifin, idan ya sulala sai Ki sauke Ki dora tukunya Ki zuba ruwan kadan Ki zuba man gyada Ki sai Ki dauko attaruhu Ki jajjaga sai Ki zuba a cikin tukunya da ke kan wuta.
Sai kayan kamshi zaki dauko Ki zuba a ciki sai Ki bari sai ya soma kamshi sai Ki yanka albasa Manya Ki zuba sai ya dau kamshi sosai ko mai da kika saka ya dahu sosai sai Ki dauko alayyahu Ki tsince mai kyau Ki zuba ki wake Ki zuba amma karki bari ya dahu yar uwa zaki sha mamaki.
Comments
Post a Comment