Main menu

Pages

YANDA AKE HADA YOGHURT DOMIN SIYARWA KO AMFANI A GIDA

 Yadda Ake Hada yoghurt a gida don siyarwa ko amfanin cikin gida.


Abubuwan da za a nema idan za a hada wannan yoghurt sun hada da;

1. Madara ta Gari. (wadda baa sama evarporated milk ba)

2. Sodium

3. Flavour

4. Sugar


Wadannan kayan dasu ake hada VIP Yoghurt mai madara zallah. 


Da farko za a samu tukunya a samu ruwa kimanin liter 2 da rabi sai a juye liter daya a tukunya asa wuta har sai ya tafasa.Sai a dauko madara kamar gwangwani 4 a juye a sauran ruwan nan wanda aka rage liter 1 da rabi kenan sai a kwaba madaran sosai har sai an tabbatar babu kulu ko kadan an murje ta ta zama ruwa.
Sai a dauko tafasasshen ruwan nan a juye a ciki sai a motsa a rufe a barshi yayi away 24 kwana daya kenan.Sai a bude idan ta kwana,  a zuba sugar da flavour da sodium a motsa. sodium kar yakai rabin cokali shi kuma flavour a nemi mai kamshin madara shima kar ya wuce rabin chokali a motsa sosai ita kuma sugar ya danganta da yanayin son zakin da ske so sai a auna karanci kasa da gwangwani 4 zuwa abinda yasamu ana yi ana testing har a tabbatar da yawan zakin da ake so.In akai haka an gama sai a samu robobi ko leda a kulla sai a saka a fridge yayi sanyi a sayar a kai kasuwa.Idan Kuma an yune don amfanin gida to idan yayi Sanyi sai asha ko a dama fura duk dai abinda akeyi da Yoghurt to zakuyi da wannan.Akwai hadin da kila na samu lkci nayi wanda ake sa ticner da sweetner. amma dai ku fara yin wannan.Kabiru Muhammad Da fatan na cika alkawari. ya kamata kaima ka fara posting anan amma in sun fara turo pics na tabbacn sunayi din ngd

Comments