Main menu

Pages

YADDA ZAKI HADA TURAREN WUTA NA DAKI, HADA NA MUSAMMAN




Yadda Zaki hada hadadden Turaren wuta na daki Hadi na musamman da Matan Aure kadai zasuyi amfani dashi.


Turaren wuta na daki wanda ke tafiya da kowanne zamani da kowacce Mace Amarya ko uwar gida matukar tanason miji ya zama me zumudin zama a dakinta tareda zumudin dawowa dakinta, kai wannan shine turare da matan aure kadai ke yinsa.




Suma akwai sharadi sai wanda sukeda tabbas akan miji ne kadai zai shiga dakinsu domin wannan turaren dakin ba'a sakashi a lokacin abari wani ya shiga dakin koda kuwa 'yar uwaki ce mace, shiyasa akeso kada kisaka sai da dare kafin miji ya dawo saiki saka shi kamar yanda zakiyi turaren wuta, zaki turara dakinki dashi,




Ingantaccen hadine Wanda Zakiyi mamakin yanda kamshinsa ke canjawa a daidai lokacin da kika saka shi, amma ki fara lura da kayan hadin wanda suke canja kamshinsa wanda bayaga itatuwan turaren wuta kamarsu;

- Sandal

- Hawi

- Gab-Gab

- Durot

- Ouhd

Duka wadannan kowanne zaiyi sai kuma madarar turare shima kowanne za'asamu ya zama me kamshi sosai, wanda kamshinsa bazai damu mijin kiba wadannan sune ake fara hadawa da farko.




Sai kuma asalin maganin wanda su kuma itatuwan ake garinsu ana hadawa dashi turaren wutan amma anaso ya zama yawansu daya kada garin maganin yafi turaren yawa. Ga abubuwan da zaki nema

- Tsaiduwa

- Furen rumfu

- Furen tunfafiya

- Kafi Malam

- Ganyen Dan mannau

Shine turare dake Hana miji doguwar hira haka zalika ya hanashi Zama a turaka shi kadai kamshinsa kadai ya isa ya tada hankalinsa izuwa gareki.

Comments