Main menu

Pages

BABBAN BANKIN NAJERIYA CBN YA KARA WA'ADIN KARBAR TSOFAFFIN KUDI

 



Babban Bankin Nigeria CBN ya Kara wa'adin karbar tsofaffin kudi, bisa sahalewar Shugaban kasa.

Babban bankin Najeriya CBN ya sanar da ƙara wa'adin daina karɓar tsofaffin kuɗi zuwa 10 ga watan Februare.



Gwamnan babban bankin Godwin Emefele ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi.



Gwamnan ya ce ya zuwa yanzu CBN ya karɓi naira tiriliyan 1.9 na tsofaffin kuɗi, saura kuma naira biliyan 900 ya kammala karɓar tsofaffin kuɗaɗe.



Ya yi bayanin cewa sai da CBN ya nemi sahalewar Shugaba Muhammadu Buhari domin ɗage wa’adin karɓar tsofaffin kuɗin, wanda kuma ya amince a ƙara wa’adin da kwanaki 10.



“Sakamakon halin da ake ciki, mun nemi umarnin kuma mun samu daga shugaban ƙasa kamar haka: ƙarin kwanki 10 na karɓar tsofaffin kuɗi daga 31 ga watan Janairu zuwa 10 ga watan gobe na Fabirairu, za a ci gaba da karɓar kuɗin daga hannun ‘yan Najeriya a hukumance,” in ji sanarwar.




"Dama ta kwana bakwai, daga 10 zuwa 17 ga watan Fabrairu, domin al’umma su iya kai tsofaffin kudadensu Babban Bankin Najeriya bayan cikar wa’adi, kamar yadda doka ta 20(3) da ta 22 ta Babban Bankin ta tanada".




“Bayanan da muka samu tun daga 2015, sun nuna kuɗaɗen da ke yawo a hannun ‘yan Najeriya sun kai naira tirliyan 1.4. Amma ya zuwa watan Oktoban 2022, alƙaluma sun nuna akwai sama da tirliyan 3.23 da ke yawo a hannu mutane. 




“Wannan na nuna a naira biliyan 500 kacal a hannun bankuna, yayinda naira tirliyan 2.7 ke boye a hannun wasu ƙalilan.”



Gwamnan CBN ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su zama masu biyayya da haɗin kai wajen tabbatar an gama mayar da kuɗaɗen ba tare da wani tashin hankali ba.



Gabanin wannan mataki dai, da dama daga cikin ‘yan Najeriya sun fuskanci yanayi mara daɗi wajen mayar da tsofaffin kuɗaɗensu zuwa bankuna.



Cikin sanarwar gwamnan Babban Bankin ya yaba wa Shugaba Buhari na haɗin kai da ya bai wa CBN domin gabatar da wannan sauyin kuɗin wanda ya ce “ya kamata a riƙayi duk shekara 5 zuwa 8, amma Najeriya yanzu ta shafe shekara 19 ba ta sauya nata kuɗaɗen ba".

Comments