Main menu

Pages

YADDA ZAKI HADA SABULUN KANKANA DOMIN GYARAN JIKI

 



Yadda Ake Hada Sabulun Kankana na gyaran jiki, din sana'a ko amfani a gida.


Kayan da ake bukata sune kamar haka.

1. Caustic soda

2. Soda ash

3. Palm kanel oil (pko)

4. Silicate starch

5. Colour

6. Turare

7. Ruwa

8. SLS

9. Kankana



Yadda ake hadawa shine zaka samu KANKANA ka markada ta ka zuba mata ruwa da ruwan kankanar da ruwan daka zuba duka kada ya wuce yawan gwangwani 5.

 Saiku tace ya zama zallah ruwan kankanar

Saiki dauko  roba ki zuba caustic soda gwangwani 1 saiki sa ruwan kankana gwangwani 3.




Saiki jika soda ash Rabin gwangwani sai sls 1/8 na gwangwani ki motsa su saiki sa masu  ruwa gwangwani 2. 



Zaki barsu suyi a kalla 24hours musamman caustic soda ita soda ash ba lallai sai sunyi 24 ba koda 5hr suka samu ya isa.




Zaki rinka motsa su a ruwan su narke ki tabbatar sun narke sosai sannan ki rufe ki barsu su cika wa'adinsu, saboda idan basu narke ba kwantawa suke akasa kuma bazai maki abinda kike so ba.



Washe gari bayan sunyi saiki dauko pko dinki wato palm kanel oil saiki motsa shi ki zuba gwangwanin silicate a ciki ki motsa sannan ki zuba turare ki motsa saiki samu colour red kisa yar kadan ki motsa sosai.




Sannan saiki tace ruwan caustic soda saiki juye a wani roba mai kyau haka shima soda ash sannan saiku juye taceccen ruwan caustic soda a cikin hadin pko ki motsa sannan saiki dauko na soda ash shima ki motsa.




Zaki motsa sosai sosai sannan saiki samu robobinki ki juye shikenan  ki bashi wasu mintuna zai bushe ya zama sabulun KANKANA. 



Note: duk a taceccen ruwan KANKANA dinnan zaki dibi ruwan da kike bukata.


Sannan kowanne aka zuba a tabbatar an motsa kafin a zuba na gaba.

Haka zalika wajen juyawar anaso kayi clockwise ko anti clockwise ba aso kaita juyawa yadda kakeso.


Da fatan za a jaraba

Comments