Main menu

Pages

YADDA ZAKI HADA SABULUN YIN TSARKI MAFI KYAU DA INGANCI

 Yanda zaki hada hadadden Sabulun yin Tsarki mafi inganci, madadin yin amfani da kowane irin sabulu.


Ba kowane sabulu ne ya dace mace ta rika wanke gabanta da shi ba saboda yawanci sabulun suna haddasa matsaloli a gaban mace sakamakon karfin da suka yi ma gurin.

 Ruwan dumi shine ruwan da ya kamata kina kama ruwa da shi. Ko da haihuwa kika yi kada ki yi amfani da sabulun DETTOL ko ruwan sa domin yana kashe kowacce kwayar da take cikin farjin mace kin san kuma farji akwai kwayoyin cuta akwai masu amfani amma shi dettol dukkansu zai kashe, sai dai balaifi in akwai kuraje a gurin.
 Ki kula lokacin da zaki kama ruwa sai ki samu ko towel mai tsafta sannan sai ki tsane gun sannan sai ki mayar da pant dinki amma idan kina mayarwa da ruwa a jiki shima sai ya jawo miki kaikayi ko warin gaba.
 Ki rika yawan canja pant kamar sau 3 a rana musamman lokacin zafi, kada ki bari iska tana shiga farjinki, ya kamata idan zaki yi jima'i a rika rage iskar fanka ko AC, ga yanda za ki hada sabulun.


 - Sabulun zaitun

- Bagaruwa

- Farin miskiu

- Man Hulba 

- Sabulun saloZaki daka bagaruwarki tayi laushi sai ki goga sabulunki a gun abun goga kubewa sai ki hada da wannan bagaruwa ki zuba farin miski da man hulba sai ki cakude su ki samo roba mai kyau ki zuba ki rinka kama ruwa dashi.
 Amfanin wannan sabulun zai kashe miki kananan cututtuka masu ragewa farji dadi sannan zai sanya ki matse.

        

Comments