Main menu

Pages

BAYANI AKAN FIBROID, ALAMUNSA, DA YADDA ZA A MAGANCE SHI

 



Cikakken bayani akan Fibroid, da Alamomin da akeji idan har ana dashi da yadda za a Magance shi a likitance.

Menene "fibroid"? Fibroid (الورم الليفي) wata matsalace a mahaifar mace, wato wani yanayi ne da wani curin nama yake fitowa  kuma yana girma a mahaifar mace. ƙululun naman mai cutar da lafiya  yana ɗanfare da wani sashen mahaifar (uterus) da wasu igiyoyinsa matakam. 




" Fibroid" kalmar turanci ce, domin sauƙin furuci da Hausa, zamu cigaba da amfani da lafazin FAIBIROD a cikin bayanin mu anan . Anyi ƙiyasi cewa cikin mata 100, kashi 20 zuwa 50 na matan suna da fibroid, musamman a shekarunsu na samun haihuwa - wato daga shekara 16 zuwa 50.




 Wani ƙiyasin kuma ya nuna cewa mata 30 zuwa 77 suna samun matsalar fibroid a lokacin shekarunsu na samun haihuwa, wato lokacin ƙuruciyar balaga zuwa lokacin tsayawar al'adar mace saboda manyanta ko tsufanta (menopause).




Mafi yawan nau'in faibirod da ake samu baya da alaƙa da ciwon-daji / kansa (not cancer). ƙululun ko ƙwallon irin wanda baya da nasaba da ciwon-daji ne (benign/non-cancerous). Yana iya fitiwo fiye da ɗaya a mahaifa, kamar guda uku, huɗu koma fiye da haka a wurare daban-daban cikin mahifa.





To ta ya za a gane alamomin matsalar Fibroid?

Wasu daga cikin alamomin sun haɗa da:

1. Zubar jinin al'adah mai yawa, ko na tsawon lokaci

2. Zubar jini a baƙin lokutta ko tsakanin lokuttan haila

3. Ciwon ƙugu, saboda ƙululun yana danne wani sashen jiki cikin mahaifa

4. Yawan fitsari

5. Ciwon baya daga ƙasan baya

6. Jin zafi /ciwo lokacin yin jima'i

7. Rashin jini saboda yawan zubar jini

8. Rashin jin daɗi a mara, musamman saboda girman ƙululun a ciki

9. Basur maisa tsuguno a bayi saboda rashin fitar bahaya

10. Ciwon ƙafa

11. Girman ciki kamar mace tana da juna biyu amma ba juna biyu bane, musamman idan faibirod ɗin ya girma

12. Koma rashin ganin wasu ko ɗaya daga cikin alamamomin da muka yi bayani




Matsalolin da Fibroid ke haddasawa;

- Matsala wajen haihuwa/lokacin naƙuda

- Matsala yayin fama da juna biyu

- Matsalar rashin samun juna biyu / rashin ɗaukar ciki ga mace saboda ƙululun ya toshe/taushe ko danne wani  ɓangaren mahaifa

- Yawan ɓari/zubewar ciki

  Yana da matuƙar muhimmanci mai jin ɗaya ko fiye daga cikin waɗannan matsalolin yaje asibiti   domin a binciki ko tana da matsalar faibirod ko akasin haka. Idan kuma kin riga kin sani to sai a nemi magani.





Abubuwan dake haddasa tsirowar fibroid

Har yanzu dai masana ilimi a fannin lafiya na ƙoƙarin fahimtar cikakken dalilin daya sa ake samun fibroid. Sai dai an gano cewa yawan sinadarin ESTROGEN (estarojin) a lokacin shekarun da mace ke iya samun haihuwa yana da nasaba da lokacin da mata ke samun matsalar faibirod.




 Daga shekara 16 zuwa 50 shine lokacin da sinadarin yafi yawa a cikin jinin mace. ESTROGEN ɗaya ne daga cikin manyan sinadaran jikin mace, wato ESTROGEN sinadari ne na  jinsin mace dake tafiyar da girman jikin mace, rayuwar mahaifarta da yanayin halittarta daya shafi jima'i . 




A lokacin balaga sinadarin na taimakawa yasa nonuwa da gashin mara da hammata su fito, kuma shine ke saka sha'awa ko yawan sha'awa ga mace idan yayi yawa. A lokacin balaga ƙwayayan mahaifa (ovaries) zasu fara samar da sinadarin. Za'a iya kiran ESTROGEN da suna MAƘERIN ƳAN MATA, domin kuwa shine ke taimakawa wajen sauye-sauyen halittar jikin mace yayinda take girma.




 A taƙaice, ESTROGEN shine sinadarin da faibirod suka dogara dashi domin samun daɗa girma a mahaifa, wato makamashin faibirod. Faibirod zai cigaba da girma har sai lokacin da mace ta bar yin al'ada saboda girma (menopause), daga nan sai ya fara ƙanƙancewa.





Wasu dalilai da ka iya yuwuwa mace ta samu wannan matsalar:

- Gado : Idan mahaifiyarki ko ƴar uwarki ta taɓa samun fibroid zai iya yiwuwa ki samu saboda gadon jini.


- Jinsin baƙar fata:  Mutanen Africa ko ƙasashen baƙar fata, wato jinsin baƙar fata su suka fi kowanne jinsin mata a duniya samun matsalar faibirod. Kuma matasa mata baƙar fata sune suka fi samun matsalar a shekarunsu na matasa. A ƙasashen turawa, Indiya da Chana da sauran wasu ƙasashen, ba kasafai ake samun matansu da matsalar ba.


- Amfani da hanyoyin tsaida haihuwa (ƙwayoyin tsaida haihuwa wani lokacin zasu iya sa faibirod ya girma), ƙiba, ƙarancin sindarin vitamin D, yawan cin jan-nama, rashin cin abincin ganye da yayan itatuwa,  shangiya da sauransu.





Hanyoyin da za a bi don a Magance shi

Hanyoyin asibiti na magance matsalar ya ƙunshi: aikin tiyata (surgery) domin cire ƙululun tare da cire wani ɓangaren mahaifa "uterus" [Hysterectomy] wanda zai hana samun haihuwa, sa'annan wani nau'in  aiki tiyatar [Myomectomy] wanda baya hana haihuwa a gaba, ƙwayoyin magani da wasu hanyoyin. Musamman idan ya girma aikin tiyata ne akafi yi domin rabuwa da matsalar.




Girman faibirod na iya zama kwatankwacin girman dutse karami ko ƙasa da haka, ko girman lemun tsami ko na zaƙi, ko girman ƙwallo, girman jariri koma fiye da girman jariri, musamman idan ba'a cire shiba ko magance shi ba. 



Wasu likitocin naganin idan faibirod yakai girman inci 4 (4 inches/9-10 cm) to akwai buƙatar ayi aikin tiyata domin a cire shi.

Comments