Main menu

Pages

ALAMOMIN BUDADDEN GABA, DA HANYOYIN DA ZA ABI DON TSUKE SHI

 Cikakken bayanin matsalar budewar gaba, alamomin budadden gaba da yadda za ayi don tsuke shi.


Yanayin halittar farji tamkar robar danƙo ce wacce zata iya buɗewa idan aka yi mata talala, haka kuma  zata iya komawa ta haɗe, wato ta  tsuke bayan buɗewa. Tsokokin bangon  farji masu motsi ne kuma zasu  iya tsukewa ko buɗewa idan mace tayi yunkurin tayi hakan, wato idan ta motsa su ko matse su ta ciki.
Buɗaɗɗen farji (loose vagina) ko buɗewar farji (vaginal looseness) wani yanayi ne dake shafar mata da yawa musamman lokacin juna biyu da kuma bayan haihuwa inda farji ke canza yanayin halittarsa  ya ƙara girma, wato ya zama buɗaɗɗen wuri kasancewar naman dake zagaye da farji mai yin zobe lokacin jima'i ya saki, tsokokin sun saki basu iya riqeshi yanda ya kamata lokacin saduwa. 
Kamar dai yanayin halittar fatar jikin mutum, wasu mutanen fatarsu nada tauri  kamar roba marar sauƙin buɗewa idan aka jata,  wasu kuma fatarsu nada laushi da sauƙin yin talala idan aka jata, kusan haka itama halittar  gaban mace take. 
Wurin haihuwa jinjiri na fitowa ne ta farji inda wurin ke buɗewa sosai domin jinjiri ya fito. Bayan wani lokaci da haihuwa  farji na komawa ya tsuke . Duk da haka, farji ba zai taɓa komawa ba kamar yanda yake ada ko kamar na macen da bata taɓa haihuwa ba (ko budurwa), koda kuwa anbi hanyoyin magani, farji zai zamanto ya ƙara  girma kaɗan ko da yawa.

Yawan haihuwar mace, buɗewar gaba saboda tiyatar likita/ƙarin ƙofa a lokacin haihuwa (tear) da yawan yin jima'i yau da gobe, na daga cikin dalilan dake haddasa buɗewar gaban mace. Idan buɗewar farji tayi yawa  yana zama ƙalubale ga ma'aurata.
 Zaya iya zama matsala a rayuwarsu ta jima'i. Saboda wannan yanayi na sanya raguwar ɗanɗanon jima'i ga mace da mijinta koma ya hana macen jin ƙoluluwar daɗi  (orgasm) lokacin saduwa. Dalilin faruwar haka shine,  farji baya matse/riƙe ayabar da  kyau, ta yanda za'a samu ɗanɗanon gugar fata-da-fata tsakanin ma'aurata biyu wanda jin  wannan guga shine  zai kai ma'auratan biyu  ga gamsuwa mai ƙarfi a lokacin jima'i.
Bugu da ƙari, wannan matsala  na iya saka mace cikin damuwa da jin cewa bata amsa sunanta na cikakkiyar mace ba saboda bata jin daɗin saduwa kuma bata iya gamsar da mijinta da kyau. Hakan kuma zai iya sanya maigidan ya ƙara wani aure domin biyan buƙatarsa. 
Hakika gamsuwar aure itace saduwa mai daɗi tsakanin ma'aurata da zata samar da soyayya da zaman lafiya mai  ɗorewa. Matsattsen gaba (tight vagina) bakin gwargwado, yanayi ne mai kyau da zai iya ƙarawa mace gishirin  soyayya mai ƙarfi tsakaninta da mijinta.
Yanda zaki gane cewa kina da wannan matsala ta budewar gaba.

1. Mafi yawan mata masu fama da matsalar buɗaɗɗen gaba na fama da matsalar rashin riƙe fitsari, wato ɗigar fitsari. Digar fitsarin zata iya faruwa a lokacinda kika ɗauki wani abu mai nauyi, ko lokacin da kika yi dariya, tari, ko atishawa. Wannan alamace ta cewa mace nada buɗaɗɗen gaba.Yawan shekaru, yawan haihuwa, yawan jima'i, tiyatar likita (ƙarin ƙofa) ko wani rauni a  gaban mace, ko   tsayawar al'ada (menopause) saboda ƙarancin sinadarin "estrogen" na iya sanya raunin tsokokin farji wanda daga ƙarshe zai iya haddasa buɗewar tsokokin bangon  farji masu matse ayaba.
2. Hanya ta biyu da zaki iya sanin ko kina da gaba mai faɗi itace: ki saka ɗan yatsanki guda (manuni) cikin gabanki sa'annan kiyi ƙoƙarin matse dan yatsan da tsokokin farjinki.  Idan har kika gwada yin hakan kuma ya zamanto baki iya jin kina matse dan yatsan da farji to zaya iya zama kina da babban wuri. Bugu da ƙari, idan kika saka yatsa 2 ko 3, misali manuninki da kuma yatsan tsakiyar hannnunki (mafi tsawo), kuma baki ji wata alamar bangon farjinki yana matse yatsun ba to yiwuwar itace kina da buɗaɗɗen farji.
3. Idan ya zamanto yana da wuya kamin kiji ƙololuwar daɗi (orgasm)/kawowa lokacin saduwa. Yana iya yiwuwa alamar buɗaɗɗen gaba ne. Haka kuma, raguwar jin daɗi ba kamar da ba shima na iya zama alamar.
4. Idan ya zamanto mace tana wasa da gabanta domin biyan buƙatarta kuma tafi sha'awar ta saka wani babban abu a gabanta akan ƙarami - wato bata jin daɗin ƙaramin abu idan ta saka a farji sai babba. Shima alamace cewa mace nada girman farji.  A baya munyi bayani da tsoratarwa akan wasa da gaba. Yana da illa ga lafiya da rayuwar auren ƴa mace. Don haka sai a kiyaye.5. Idan ya zamanto kina shan wahala kafin ki gamsar da mai gidanki wajen jima'i ba kamar a baya ba.
6. Idan ya zamanto sai kin matse ko haɗe cinyoyin ki biyu  sosai sa'annan kike jin daɗin jima'i da maigidanki. Wannan ma yana iya zama alamar buɗaɗɗen gaba. Duk da dai cewa wani lokacin yana iya zamantowa mijin ne keda ƙaramar al'aura. Amma idan kafin haihuwarki babu wannan matsalar sai daga baya to sai ki zargi buɗewar gaba.
7. Idan ya zamanto kina jin ƙarar fitar iska daga farjinki lokacin da maigidanki yake saduwa dake, iskar kamar fitar "tusa" amma ba tusa bace (fanny farting) kuma babu wari. Iskar yana shiga yana fitowa  lokacin da maigida yake kaikawo. Wannan alamace kina da buɗaɗɗen farji.

Hanyoyin da za abi domin tsuke Farji

Akwai hanyoyi da dama na matse gaba musamman bayan haihuwa wanda sun haɗa da hanyoyin magani, motsa jiki (exercise), tiyatar likita domin rage girman farji da sauransu. Wasu hanyoyin nada illa ga lafiya, wasu kuma hanyoyin basa da wata matsala ko haɗari kamar dai yanda likitoci ke bayani. Wasu daga cikin hanyoyin:


1. Motsa jiki: Hanyoyin motsa jiki na zamani domin matse gaban mace suna da yawa (such as kegel exercises) da sunaye. Motsa jikin ya shafi horo da mace zata iya bawa jikinta domin ya zamanto tsokokin gabanta masu motsi sun kara ƙarfi da tsukewa. Misali, wata ƙwararriyar likita a India Dr. Sangeeta Gomes ( Consultant Obstetrician and Gynaecologist) , ta nuna cewa mace zata iya inganta tsukewar gabanta idan tana yin motsa jikin ɗauke numfashi (breathing exercises). 
Zaki ɗauke numfashinki na tsawon 'yan daƙiƙoƙi (seconds) kaɗan sannan ki tsuke (tsokokin) farjinki matakam na tsawon wani lokaci a lokacinda kike mai ɗauke numfashin. Za kiyi hakan a kowanne wuri ba tare da ma wani yasan abinda kike yi ba. Sa'annan  zaki yawaita cin Ƴaƴan itatatuwa (kayan marmari) da abincin ganye (vegetables). Wannan ko shakka babu zai taimakawa  mace wajen matse gaba domin gyara aurenta.

Wani nau'in motsa jikin kuma shine ake cema "Kegel exercise". Toh  yaya ake yinshi? Dr. Gomes ta nuna cewa idan kina yin fitsari sai ki tsaida fitar fitsarin, wato ki  riƙe fitarin, ki danne shi na tsawon daƙiƙoƙi 10 , wato ki ƙirga 1 zuwa 10 sa'annan ki saki fitsarin a hankali a hankali. Zaki iya yin hakan sau 2 ko 3 a rana idan za kiyi fitsari. Shima wannan nau'in motsa jikin na tsuke gaban mace.
2. Hanya ta biyu shine wanke gaba da ruwan sanyi mai ƙankara: Yana  taimakawa  wajen matse gaba amma sai an haɗa da motsa jikin da muka yi bayani. Wannan yana daga cikin hanyoyin da Dr. Gomes ta zayyana. Amma zaifi dacewa ace sai mace ta gama wankan jegonta na kwana 40 kwata kwata sa'annan tayi amfani da ruwan sanyin, wato bayan ta koma "normal". Saɓanin yanda al'adar Bahaushe tayi imani dashi cewa ruwan sanyi na lalata gaban mace,wasu likitocin a wasu al'adun na ganin yana matse gaba.
3. Yin amfani da aluf (alum). Aluf yana matse gaba sosai sai dai likitoci na tsoratarwa akan yin hakan saboda da sinadarin kemikal ne. (Chemical)
4. Yin tiyatar likita domin rage buɗewar farji. Wannan ma hanya ce ta zamani amma ana tsoratarwa akan yin hakan saboda wasu dalilan lafiya.
5. Yunƙurin tsuke gaba a lokacin saduwa, wato ki matse farjinki ta ciki lokacinda mijinki yake kaikawo. Zaki yawaita yunƙuri domin tsuke gabanki domin mijinki yaji alamun ana riƙe masa al'aura tamkar zobe zagayen gabansa. Idan mace na yawaita yin haka to zai zama ɗabi'arta kuma nan gaba ba zata san ma tanayin hakan ba saboda ta riga ta horar da jikinta, kuma hakan zai inganta jin daɗin mijinta sosai. Allah Ya taimaka.

Comments