Main menu

Pages

YADDA ZA A MAGANCE MATSALAR RASHIN KUZARI GA MACE KO NAMIJI

 Yadda za a Magance Matsalar rashin Kuzari ha Mace ko Namiji cikin sauki Insha Allah.


 Ina mata da maza wadanda  kuzari bai ishe suba sannan kuma ba sajin karfin jikin su to wannan wata da mace ta samu idan kuna san samun kwari da kuzari sai kuyi wannan hadi ku gani.

- Dabino

- Nonon Akuya

- Zuma

- Citta Za a sami dabino mai kyau a tabbatar an gyara saboda yawancin dabino ana samun kwari aciki.
 Nonon akuya ana so dole sai kin samo na akuya so samun a gabanki ko gabanka za a tatsa idan an samu nonan sai ki zuba dabinon da kika gyara acikin nonan akuyar ana bukatar ya samu kamar awa goma idan da hali kiyi da dare ya kwana da safe.

Dabino ya jika acikin nonon akuyar ana so kikai ki markade amma karki zuba ruwa acikin markadan idan kin gama sai ki dauko zumarki amma anfi san farar saka sai dai in baki samu ba sai kiyi da ko wacce, kizuba zumar aciki ki juya.

Ita kuwa citta garinta zaki samu mai kyau wanda kika san babu wani mix aciki ko ki daka abinki yafi sauki 'yar uwa kina shan wannan hadi ko kana shan wannan hadi zaku ga yadda kuzari zai samu da yarda Allah.

Comments