Main menu

Pages

AMFANIN RIDI GA LAFIYAR MACE DA YADDA YA KAMATA TA SARRAFA SHI

 



Amfani Ridi ga Lafiyar Mace da yadda ya kamata tayi amfani dashi.


Ba abunda ke gyara jiki naci in ba kayan itaceba fruit saikuma cin danyen tomatir da cucumber kina cinsu inkin yanka sai kuma zogale ki markada kina shansa da madarar luna sai ki kiyaye shiga rana sannan ki tafasa ruwan kaninfari da xuma kina sha yana saukar da ni’ima ga gyara fata...




Yawanci ba kowa ba ne ya san alfanunsa ba. Yawanci Hausawa ba su cika damuwa da shi ba, sai wasu ƙabilu dake maƙwabtaka da su. Riɗi daga darajarsa ya kamata mu fahimci lallai yana ƙunshe da amfani mai yawa ko ga zakkarsa idan muka duba. Riɗi yana da amfani mai yawa a jikin mace da namiji.




Ga Mace yana mata matuƙar amfani ga mahaifarta, don yana wanke dattin mahaifa, da rikirkicewar al’ada.Yana kuma saka mace saurin ɗaukar ciki, da samun lafiyar mahaifa da rigakafin kamuwa da ciwon dajin mahaifa da sauran wasu cututtukan da suka shafi mata. Yana saka jikin mace ya daina bushewa da taushin fata.




Idan za kiyi amfani da riɗi wajen neman lafiya,to aƙalla ki yi kwana biyu kina aikinsa, kafin ki kai ga samun garinsa yadda ya kamata. Da farko za ki gyara Riɗinki ta hanyar wanke shi sai ki bar shi ya bushe, sannan a niƙa shi zuwa gari. 




Za kiga ya dunƙule saboda yana da mai, sai ki baza shi ya ƙara bushewa, sai ki zuba a turmi, harki samu ya warware. Sai ki riƙa ɗiba kina sha a nono, ko ki ci shi haka nan. Amma ana so ki ɗan ba shi tsoro da wuta




Na biyu kuma kina iya samun ƙwai kamar guda uku, ki fasa su, ki samu tumaturi, manya guda uku, ki zuba dafaffen zogale a matsayin albasa, ammah ya fi albasar da kike sakawa yawa. Ki sa Maggi, Gishiri yaddah ki ke so, ki juya, sosai sannan ki soya. 




Suyar ba za ta kafe ba, za ta dagargaje, ta yi miki ruwa-ruwa, ki zauna ki cinye. Idan kina da madarar shanu, ki dora a kai. Idan babu ki sami kamar Yoghurt ko nonon shanu, ki ƙara masa ruwa, ya yi tsululu, ki sa Suga ko zuma kaɗan, ki juya sannan ki shanye.




Irin waɗannan abinciccikan suna da kyau mata su riƙa amfani da su a kowane lokaci.


Haka ma Ƙwai, kamar yadda kowa ya sani ne cewa dafaffan ƙwai ya na ɗaya daga cikin nau’o’in kayan abincin da ke gina jiki. Kazalika da yawa daga mutane ba su san cewa ƙunduwar dake tsakiyar ƙwai ta fi farin da ke kewaye da ita fa’ida a ɓangaren gina jiki, ƙara lafiya, kuzari tare da sanya ƙwarin jiki ga ɗan Adam.




Da akwai labaran ƙanzan kurege da aka jima ana yayatawa, cewa wai duk wanda ke cin ƙunduwar ƙwai akwai yiwuwar ya kamu da ciwon zuciya, wannan dalili ne ya kan sa wasu mutune ya cire ƙunduwar ƙwan sun yasar a sau da dama, sannan su cinye ragowar farin dake kewaye da ita.




Dangane da wannan jita-jitar ne ya sanya ni sha’awar tantancewa tare da fitar da gaskiya dake tattare da lamarin ta hanyoyin binciken da masana lafiya a duniya suka fitar.




Kamar yadda binciken ya nuna, cin dafaffen ƙwai tare da ƙunduwarsa baki ɗaya, ya na matuƙar rage ƙiba tare da sanya ƙoshin lafiya. Saboda haka, yasar da ƙunduwar ƙwai ba dabara ba ce, idan aka yi la’akari da irin rawar da take takawa wajen gina jiki da kuma ƙara ingantacciyar lafiya ga jikin bil-Adama.




Haka zalika, kai tsaye za a iya cewa, cin dafaffen ƙwai a matsayin karin kumallon safe ga ɗan Adam, na yin tasiri ta yadda duk wani abu da aka ci wadda ke sanya ƙiba, to ko kaɗan a wannan ranar ba zai yi tasiri ba.




Har ila yau a wani binciken da aka gudanar a ƙasar Amurika, ya nuna cewa, waɗanda ke amfani da dafaffen ƙwai a matsayi karin kumallon safe ba za su taɓa zama ɗaya da waɗanda ba sa yi da shi ba, ta fuskar rage ƙiba, tare da sanya kuzari da kuma yalwata lafiyar jiki baki ɗaya.

Comments