Main menu

Pages

YADDA ZA A MAGANCE TSAWAITA NAQUDA GA MACE MAI CIKI
Abubuwan da Mai Juna biyu ya kamata tayi lokacin da cikin ya tsufa don don magance tsawon naquda.


Tabbas mata da yawa sukan sha wahala sosai idan watan haihuwarsu ya kama domin Allah kadai Ya san irin yanayin da suke shiga. Wannan shafin mai albarka, ya kawo maku wata fa’ida  wacce tabbas mun tabbatar da ingancin ta idan aka jaraba in sha Allah za a dace duk wata mace mai shan wahalar nakuda to ta samu Zuma mai kyau kaman cikin Kofi ko cokali 24 ta shanye a take.                                                                                                                                             
Sannan a samu wani zumar a zuba ruwan zafi a ciki tana shan shi da zafi wannan zai taimaka wajen juya yaro in sha Allah. Hakan yama fi ruwan nakuda karfi, Sai dai kuma in Allah bai yi fitar yaron ba a lokacin amma inba haka ba a take yaron zai fito insha Allahu. 
Shiyasa yana da kyau sosai da zarar cikin mace ya kai wata 7 ta dinga tafasa ‘ya’yan hulba tana zama a ciki kullum sau daya in ya shiga wata 9 ta dinga yi safe da yamma. Hakan zai taimaka sosai wajen bude kofofin aihuwa kuma da wuya mace ta karu a lokacin aihuwa. 
Kuma mace za ta samu garin hulba ta kwaba da Zuma tana shan cokali biyu safe da yamma, insha Allahu  za ta samu sauki sosai wajen haihuwa amma kada mace mai ciki ta yi amfani da hulba har sai cikin ya tsufa ma’ana lokacin nakuda saboda hulba tana zubar da yaron ciki. 
Allah Ya sa mu dace dan Allah duk wanda ya karanta to ya yi kokari ya sanar wa yan’uwa mata saboda a samu saukin nakuda sannan kuma a samu saukin fitar yaro daga cikin mahaifa. 

Comments