Main menu

Pages

YADDA ZAKI YI AMFANI DA DANYEN MAN KWAKWA DON MAGANCE TUMBI DA NANKARWA

 



Yadda Zaki sarrafa Kwakwa ki fidda Man don magance Tumbi da Nankarwa.


A wannan satin, za mu bijiro da amfanin man Kwakwa wajen warkar da wasu matsalolin da ke damun mata, wadanda suka hada da rage tumbi da warkar da nankarwa, wato ‘Stretch mark’ a Turance.




A kan samar da danyen man kwakwa ba tare da kona wani abu daga amfaninshi ba. Ba shi da wahalar hadawa, ba a bukatar yin amfani da wuta, kamar yadda na fada a baya.

 

 

Da farko, uwargida za ta samu kwakwa daidai bukata, sai ta cire bawonsa, ta yayyanka su kanana, sannan ta markade sosai. Bayan kin markade, sai ki tace ruwan, ki dura a roba, sannan ki ajiye shi a wuri mai iska, ki bar shi ya kwana.



Da safe za ki ga mai ya taso a sama, ki sa cokali, ki yade man, ruwan ne kadai zai rage a kasa. Za ki gan shi kamar man shanu, in kuma kina bukata, kafin ki yade man, sai ki saka shi cikin firji don ya yi kankara. Hakan ya fi dadin yadewa, za ki gan shi kamar man kade. Masana sun tabbatar cewa ya fi dafaffen man kwakwan tasiri.




An nuna cewa za a iya shan shi haka nan domin rage tumbi. Baya ga wannan, za a iya amfani da shi wajen magance Amosanin kai, wato ‘Dandruff,’ don haka za a iya amfani da shi a matsayin sinadarin wanke kai (Shampoo). Ko kuma a hada shi da man kitso da man shafawa domin gyaran jiki matuka.




Ta bangaren warkar da nankarwa kuwa, babu kamar man kwakwa. Da zaran kika fara amfani da shi wajen shafawa a jikinki, tabbas za kiga nankarwa ta fara bacewa.




Don haka a takaice kwakwa da manta suna da matukar amfani ga mace, baicin wadannan da muka lissafa. Ruwan na magance wasu cututtukan jiki, musamman masu cututtuka a mafitsara, wanda ake kira a Turance ;Urinary infections.’



Allah ya ba mu sa’a, Allah ya taimake mu, da fatan za a wuni lafiya, kuma a rika kula da yara yadda ya kamata. Mu hadu a wani makon.


Comments