Main menu

Pages

YANDA ZA A MAGANCE YAWAN AMAI KO TASHIN ZUCIYA GA MAI CIKI

 



Yanda za a Magance Matsalar yawan Mai ko Tashin zuciya ga Mace Mai ciki.

Matsalar amai ko tashin zuciya ga mata masu ciki matsaloli ne dake haifar da damuwa ga mata masu ciki. Juna 2 na daga cikin ababen dake sa yawan tashin zuciya, zubar da miyau dama aman musamman aman safe. 




Dan magance wannan yanayin akwai dubaru uku dana fito dasu wadanda ka iya magance matsalar a samu sauki.


1- Amfani da magunguna na prenatal vitamins magunguan da ake sha na mata masu ciki na matukar tsakaita amai da tashin zuciya.




2- Amfani da magungunan tsaida amai da tashin zuciya wadanda ake iya anfani dasu lokaci zuwa lokaci daga likita idan bukatan hakan ta taso.




3- Kaucewa sha ko anfani da duk abunda akasan yana tada zuciya ko sa amai kamar abinci, magani da sauransu. 


Har ila yau Kuma, ga masu yin aman safe musamman mata masu ciki dake yawan aman safe. 


A rika anfani da toast, cereal, crackers, ko sauran dry foods kafin tashi daga gado.


A rika anfani da cheese, lean meat, ko kuma sauran high protein snacks kafin kwanciya dama shan fruits.


Allah Ya ba dukkan Musulmi mara Lafiya, Lafiya, masu ciki Allah Ya sauke ku Lafiya.

Comments