Main menu

Pages

YADDA WATA BUDURWA TA RASA RANTA A WAJEN KIDAN DJ

 Tirkashi yadda wata budurwa ta rasa rayuwarta a wajen kidan Dj a jihar kano


Wannan ba karamin tashin hankali bane saboda idan kuka kalli abubuwan da mata suke aikatawa a duk lokacin da sukaji sautin kida zaku Tabbatar da maganar da ake cewa mara sunfi yawa a cikin wuta saboda a duk lokacin da sukaji kida sunfi kowa shagala

Itama wannan budurwa ta rasa rayuwar tana tsakiya dayin rawa acikin mutane wanda wannan abin dole a tausaya mata saboda duk wanda ya mutu acikin wannan halin kunsan ina ne makomarsa Allah yasa muyi mutuwa mai kyau
Amma dai jama’a sunyi mamaki da wannan abin saboda mutuwa ce mai cike da dinbin wa’azi acikin wanda idan mutane suna da hankali zasu lura akan wannan abin kuma ayi addu’a Allah ya kiyaye wasu
Duk wanda yaga wannan video zaiyi mamaki sosai kuma zai tabbatar da cewa Allah yafi karfin komai Babu wani abu wanda ya gagari Allah kuma za’a Tabbatar da cewa mutuwa wa’azi ce Allah yasa muyi kyakkyawan karshe amin

To sai dai ni Kam ba zan dora video ba, saboda ba zanyi shisshigi tsakanin wannan Baiwar Allah da Ubangijinta ba, Allah Gafurur Rahim ne idan Ya gadama sai Ya yage Mata, sannan dora video nata zai iya zama kamar wulaqantatane. Don haka koma dai meye mu barta ita da Wanda Ya halliceta.Wannan posting Kuma nayi shine don Jan hankali da tunatarwa ga 'yan uwa Musulmai don Musan cewa a kowane irin lokaci mutuwa na nan na kwankwasa mana Kofa.


Yaa Rabbil Izzati Ka Sanya muyi kyakkyawan karshe Ameen Ameen.


Comments