Main menu

Pages

YADDA AKE HADA MAGANIN WANKIN DAYTIN CIKI DA MARA

 Yadda za ake hada maganin wankin dattin Mara ga Maza da Mata


A nemi wadannan Abubuwa da zan Lissafosu Guda 10 wadanda duka baza suyi wahalar samowa ba gasu kamar Haka;
1. Asalin Ganyen Zaytun a dakashi ya dawo Gari sosai, a kalla ana son cikin babban Chokali uku2. Tsohuwar Tsamiya ba danyar ba, in ance Tsohuwar Tsamiya itace wacce zaka ga tayi Brown ko jah kuma tana da Danko sosai itace tsohuwar Tsamiya Guda bakwai3. Jar Gauta wacce ta Bushe kuma wacce Bata Dagargaje ba guda 74. Lemon Tsami  Guda 7 shima mekyau ba Busashshe ba5. Garin Sanamaki/Fulasko Ana samunsa a Islamic chemist, A kalla ya kai kimanin Chokali uku 3 babban Chokali6. Tafarnuwa mekyau Kwallo Uku, kuma a bare busashshen Bawonta a yayyanka ta kanana-Kanana7. Albasa Fara Babba mekyau guda daya bajaba 8. Dabino Mekyau a kalla guda 20 a baresu a cire Kwallon, a kuma cire Dattin ciki har wannan Leda-Ledar farin a cireshi9. Ganyen Zogale  busashshe kuma garin a kalla ya kai cikin chokali uku babban chokalin cin shinkafa10. Zobo, Eh zobo dai da aka sani Wanda ake jikawa yayi jah a sa siga a sha shi nake nufi, a daka garinsa shima a kalla ya kai cikin chokalin cin shinkafa uku
Sai a nemi Ruwa mai kyau a kalla ya kai kimanin Liter Biyu, ko uku, Sai a juye wadannan abubuwan da aka lissafo guda 10 din a cikin wani abu me dan girma Wanda zai dauke su, sai a barshi sai ya kwana tukunna a ciki sannan sai a juye a tukunya a dafa su su tafasa sai a tace azubashi a cikin wani Abu mekyau Wanda bazai lalata shi ba, sai a dinga sha bayan an ci abinci kullum sau biyu a yini

Ana son in aka ci abinci aka sha a tsaye sai a zauna a bubbude kafafuwa a saki jiki ana Numfashi ta yadda mara da ciki zasu sakata su wala maganin ya ratsasu sosai tsawon mintuna Goma sai a cigaba da harkokin da aka saba, da yamma ma a kara yin haka, in ana azumine kuma ana sha lokacin Sahur da lokacin bude baki (Iftihar) ana daukar kwana bakwai ne a cikin kowanne wata ana yin Service din.

Comments