Main menu

Pages

WASU DAGA CIKIN AMFANIN CIN DABINO TUN DA SASSAFE KAFIN ACI KOMAI

 Wasu daga cikin amfanin cin Dabino tin da sassafe kafin aci komai.


1-Yana warware matsalar fitar fitsari cikin ikon Allah.


2- Yana tsaftace Hanta kuma ya wanke Qoda.


3- Yana da amfani ga masu fama da ciwon tari ko wane iri ne kuwa da sauran cutukan kirji.


4- Yana kara jini mai kyau a jikin mutum.


5- Yana da matukar amfani ga masu fama da ciwon baya.


6- Idan aka daka shi akayi garinsa ana zuba cokali 2 a nono ko madara ( ta gari ko ta ruwa) ana sha, yana matukar amfani ga lafiyar ma'aurata maza da mata domin yana karfafar kowanne a cikinsu.7- Garinsa idan ana sha da Nono ko madara ( ta gari ko ta ruwa) safe da dare da ruwan zafi kadan yana matukar amfani na ban mamaki ga masu fama da matsalar low sperm count.8- Yana lalata SIHIRI kowane iri ne a jikin mutum Idan har ana cin guda 7 kullum da safe kafin ayi breakfast har tsawon wata 2 ko kwanaki 60, kuma da yardar ALLAH jikin ka zai samu tsari daga kamuwa da wani nau'in sihiri, Kambun-baka ko hassada kenan har abada sai dai wani Ikon Allah.
Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani. Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.


(Ayi mana Addu'ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.

Comments