Main menu

Pages

CIKAKKEN BAYANI AKAN SHUWAKA DA MAGUNGUNA 25 DA TAKEYI




Dogon bayani akan Shuwaka da amfani (25) da takeyi ga rayuwar Al'ummah

Shuwaka wata ciyawace mai launin kore(greenish) wacce take girma a sassa daban daban na Nahiyar Afrika dama wasu a nahiyar Turai zuwa wasu yankuna na kasashen Larabawa. A harshen Turanci ana kiranta da suna BITTER LEAF,su kuma Yarbawa suna kiranta da suna EWERU, a yayinda su kuma Igbo suke mata laqabi da suna ONUGBU.





Komai na wannan ciyawar daci ke dashi kama daga ganyenta (leaves) saiwarta(roots) da bishiyart waton (stem). Igbo suna amfani da ganyen su yi abinci musamman miya, su kuma Yarbawa sun dauki shiwaka a matsayin magani wanda suka tarar tun a zamanin kakanninsu.





A kasar Hausa musamman a arewacin Najeriya, mata masu jego su suka fi yawan amfani da shiwaka da kuma mata masu shayarwa. Amfanin wannan ciyawar ya fi gaban a nanata bawai ga mata kadaiba harta ma ga maza. Da dama abinda wasu suka dauki shiwaka kayan matane kawai. A dalili da haka yasa na zurfafa bincike akan shiwaka da kuma yin rubutu na musamman akan alfanon da take da shi ga lafiyar al'umma.





Wannan ciyawar kamar yanda na zayyano kusan komai nata daci ke gare shi, wanda hakan na karantar damu cewa rayuwa fa daci ke gareta. Mutanen da sun fi son abu mai daci fiye da abubuwan dake da zaki.





Duk da yake yawan shan abu mai daci nada illa ga jiki musamman ga hanta(liver) sai dai kuma dacin dake ga shiwaka baya illata jiki asali maganine na  wasu cutukka. Na sha jin karairayi kan shuwaka na illata jiki dan daci ke gareta, wannan ba gaskiya bane, indai an sha a yanda aka shardanta to ba wani cutarwa a tare da ita. dacin dake gareta ba irin na madaci ko dalbejiya bane.





1- Shuwaka na wanke hanta daga kwayoyin cuta, Hanta ita ce abu mafi nauyi a cikin jikin dan adam. zuqar suga da kwankwadar giya da shan magunguna barkatai na matukar illata hanta (liver).



2. Koda (kidney) wata muhimmiyar halittace dake aikin fitar da duk waste materials daga cikin jiki kamar fitsari wanda shiwaka na taimakawa koda sosai dan karfafa aikin nata.



3.Shiwaka na maganin ciwon ciki musamman ga jarirai,idan aka ga jariri yana ta wulle wulle yana tsuwa to sai uwar ta nemi shuwaka ta yi blending ta zuba ruwan zafi sai ta tace da kyau ta sha lita daya bayan awa daya sai ta shayarda jinjirinta nono,a hakika za a ga waraka da yardar Allah.




4.Diabeties-masu fama da ciwon suga shekara da shekarru to ga magani sahihi kuma mujarribun sai dai akoi bukatar bayani anan wajen sosai ta yanda za ayi amfani da shuwaka da kuna yanda za a sarrafata.




5.Idan kana fama da yawan rudewar jiki sai a sa6a ganyen ga turmi a saka ruwa a tace a tarfa zuma a sha cup daya a kullum.



6.Kasala marar misaltuwa -A nemi ganyen shiwaka a sa6e a sha liter daya da safe haka za a maimaita da yamma.Ayi haka na tsawon sati biyu.



7.Gudawa : Idan anci wani abinci wanda ya lalata ciki to a sha shiwaka.



8.Arthrities : shi ma a sha shiwaka a kullum ayi suraci da ruwan ganyenta.



9.Rashin cin abinci a koshi shima sai a sha shiwaka.



10.Gudawa ga yaranda ke shan nono a sabili da rikicewar nonon sai uwar ta tace shiwaka ta sha a sanda zata konta,haka idan gari ya waye zata sha.


11.Wankin dattin ciki


12.Maganin tsutsar ciki


13.Bayan gari mai tauri


14.Stroke-bugun jini.


15.Rashin yin bacci(Insomnia)


16.Cutukan da ake dauka ta saduwa(sexuallytransmitted Diseases ) amma banda na kanjamau dan ita Kanjamau kwayar Virus ce ba bacteria ba.


17.Kumburin ciki da zafin ciki


18.Basir mai haddasa kaikayin dubura.


19.Zafin ciki (internal heat) ko kaga kana bayan gari amma kamar na dabbobi.


20.karin ruwan nono ga mata masu shayarwa anan sai a rinka

yin kunun ganyenta ana sha.


21.Tana tsaftace nonon da ya gur6ace.sai uwa mai shayarwa ta markade ganyen tayi kununta ta sha.


22.Pneumonia da tarin sanyi


23. Cutukkan fata sai a sa6eta a shafa a wajen dake da matsalar.


24.Indigestion-rashin narkewar abincin.


25. Malaria sai a rinka sha ana suraci da ruwanta ko wanka dasu da duminsu.

Comments