Main menu

Pages

SAUKAKAN HANYOYIN DA ZAKI BI DON INGANTA NI'IMAR JIKINKI A KODA YAUSHE

 



Saukakan Hanyoyin da za ki bi don inganta Ni'imar jikinki a Koda yaushe.

Abinda mata suka kasa bambancewa da jikinsu shi ne a tunanin mace mafi yawanci "duk mace da ke da jiki mai kyau tana da ni'ima, duk mace mai danshi(juices) tana da ni'ima) aa.



Amma dole ki san jikin ki, ki karanci yanayin jikinki kamar littafi domin babu wanda ya sanki fiye da ke kanki!



Matukar level na ni'imar jikin ki ya sauka dole ki ga sauyi, babban maganin wannan matsala shine:

- Dole ki nisanci sanyi.

- Ki nisanci abu mai yawan kitse.

- Ki nisanci yawo kafa ba takalmi da zama akan tantagaryar sumunti.

- Idanso samu ne ruwan tsarkin ki kar ya zama mai sanyi. ki nisanci abubuwa masu matsanancin zaqi.

- In da so samu ne, ki mayarda kayan ganye su zama abincin ki.

- Ki mayar da 'ya'yan itatuwa su zama ruwan shanki.

- Ki koyi vegetable soup domin tana bada ma'ana!

- Ki mayar da kankana ta zama abokiyar firarki.

1- Ki mayar da kifi ya maye gurbin nama.


Comments