Main menu

Pages

HANYOYI GUDA 10 DA ZA ABI DON MAGANCE CIWON KAI KOWANE IRI

 Hanyoyi goma da za abi wajen magance ciwon Kai kowane iri ne Insha Allah.

Ciwon kai yana daga cikin ciwuka irin na yau-da-kullun wadanda suka addabi Jama'a. mafiya yawan mutane sukan yi ciwon kai Aqalla sau biyu ko uku, ko fiye da haka acikin kowanne wata.Shi yasa muka lalubo muku wasu fa'idodi Mujarrabai wadanda in sha Allahu zasu amfanar tare da taimakon Allah idan anyi amfani dasu.

1. KANUMFARI : Wanda yake fama da ciwon kai irin na Mura ko sanyi, Ko Jiri, ya nemi garin Kanumfari cokali biyu ko Uku, ya dafashi da ruwa. Bayan ya dafu sai asanya ruwan Khal cokali biyu, asanya Sugar sannan asha. Insha Allahu koda majina ce ta daskare acikin Qirjin mutum to za'a samu sauki da izinin Allah.2. KABEWA : Kabewa idan aka dafa, ka samo ruwanta ka hada da Sugar ka rika sha. Insha Allahu yana magance yawan ciwon kai. Kuma Namiji wanda yake fama da rauni wajen biyan bukatar iyalinsa, ko kuma Mace wacce take fama da matsalar daukewar sha'awa, ko bushewa zasu samu sauki.Hakanan mutumin da zuciyarsa take yawan bugawa da karfi shima idan yana shan ruwan kabewar zai samu sauki insha Allah.3. HABBATUS SAUDA : Ka samu rabin kofi na 'ya'yan Habbatus sauda, Kanumfari cokali biyu, Yansun ma rabin kofi. Ahadasu adaka aturmi. Sannan arika diban cokali biyu ana dafawa da ruwa kofi daya. Idan ya dahu sai abarshi ya huce, sannan azuba Zuma, arika sha.Masu ciwon kai, masu Olsa (Ulcer), hawan Jini, ciwon Qirji, tsakuwar Qoda, idan suna shan wannan zasu samu lafiya da izinin Allah. Za a rika sha safe da yamma ne.4. LEMON ZAQI : Asamu 'bawon Lemu ayanyanka shi kamar cikin Kofi guda, adafashi da ruwa kofi biyu. Idan ya tafasa sai asauke. Atace da rariya sannan asanya zuma arika shansa safe da yamma.

Masu Ciwon kai da masu fama da kumburin ciki ko rashin narkewar abinci zasu samu lafiya Insha Allah.5. NA'A-NA'A : Asamu ganyen Na'a-Na'a, Ganyen Raihan, a dafasu tare da kanumfari arika sanya zuma, ana shan ruwan da 'duminsa, Sannan arika goga ganyen akan goshin marar lafiyan.

Wannan maganin Ciwon kai ne sadidan, kuma yana magance cutar Kumburin jiki, Yana magance ciwon sanyi na mata, Yana magance ciwon daji (Cancer). Insha Allahu.6. SANA-MAKKIY : Cokali uku na sanamiki, Cokali uku na garin Habbatus Sauda, Cokali biyu na chitta. A hadasu adafa da ruwa kofi biyu Sannan asanya Sugar arika sha safe da yamma. Sannan arika shafa MAN CHITTA (Ginger Oil) akan goshin marar lafiyan.

Insha Allahu kai zai dena ciwo. Idan kuma Jiri ne ko hajijiya shima za'a samu lafiya insha Allah.7. MAN HABBATUS SAUDA : Arika shafawa akan marar lafiyan in sha Allahu kan zai dena ciwo. Amma za a rika maimaitawa safe da rana da yamma.
8. MAN RAIHAN : A hada man raihan da Man Hasa-lebban, tare da turaren Wardi ahada waje guda arika shafe jikin marar lafiyan baki daya. Bayan an karanta Fatiha 7, Ayatul kursiyyi 7, Suratul Fil 11, Qul Huwallahu 11, Falaki da Naasi 11 atofa acikin wannan hadin. In sha Allahu wannan maganin ciwon kai ne sosai. musamman irin wanda Shaitanun Aljanu suke haddasawa. Kuma yana magance Ciwon jiki ko shanyewar Gabobi irin wanda Aljanu ke sanyawa.9. FUREN ALBABUNAJ : Idan ana tafasawa cokali biyu, ana shansa safe da yamma kamar Tea, insha Allahu Za'a ga abun mamaki wajen samun waraka daga ciwon kai, Ciwon Qoda, rashin barci, faduwar gaba, Makalewar fitsari 

Allah Ya sa a dace.

Comments