Main menu

Pages

MUHIMMAN SIRRIKAN KARAS GUDA BAKWAI WAJEN INGANTA LAFIYARMU

 



Muhimman sirrikan dake cikin Karas, da abubuwan da yake yi ma Lafiyar mu 

 1. Taimakawa wurin kiyaye kamuwa da ciwon daji (Cancer): Karas na dauke da sinadarai masu yawa da masana ke kira 'Phytochemicals' da ke yaki da cutan daji. Wasu daga cikin sinadaren sun hada da beta-carotene da sauransu. Wadannan sinadaren na karfafa garkuwar jiki. Masana sun kuma gano karas na iya maganin Leukemia da kare yiwuwar kamuwa da ciwon daji na baki. 





2. Inganta Lafiyar Ido; Sinadarin Vitamin A yana taimakawa idanu su rika gani tangaran kuma karas na dauke da Vitamin A masu yawa. Idan mutum ya rasa Vitamin A na lokaci mai tsawo, yana iya fara samun matsala da ganinsa. 





3. Gyara fatan jiki; Karas na dauke da sinadarai masu yawa da ake kira 'carotenoids'. Binciken kimiyya ya nuna cewa 'ya'yan itatuwa da ganye suna dauke da sinadarai na ke inganta lafiyar mutum ya kuma haskaka fatarsa ya. Sai dai cin karas din fiye da kima yana iya haifar da matsala mai suna 'carotenosis' da ke saka fatar mutum tayi haske da yawa. 





4. Bugun Zuciya; Wani sabon bincike da masana kimiyya suka gudanar ya nuna cewa ruwan da aka tatsa daga karas na rage hawan jini da kashe 5 cikin 100. Sinadaren da ke cikin karas da suka hada da fibre, potassium, nitrates da Vitamin C ne ke taimkawa wurin wannan. 





5. Taimakawa masu ciwon suga; Cin abinci mai inganta lafiya yana taimakawa wurin rage kiba da kuma hana kamuwa da ciwon suga nau'i na biyu. Bincike ya nuna cewa Vitamin A na kare afkuwa da kamuwa da ciwon suga kuma tunda karas na kunshe da sinadarin sosai yana iya taimakawa. 





6. Karfafa kashi; Vitamin A yana taka muhimmiyar rawa wurin gyara kashin dan adam. Beta-carotene da karas ke dauke da shi yana kare kwayoyin hallita daga cututuka kuma yana taimakawa inganta lafiyar kashi. 





7. Cututtukan baki da hakori; Danyen karas yana taimakawa wurin kawar da kwayoyin cuta daga hakora kuma ya washe numfashin mutum. Fibre da karas ke dauke da shi yana kara adadin yawu a bakin mutum da ka iya taimakawa wajen kamuwa daga cuttukan baki.

Comments