Main menu

Pages

HANYA MAFI SAUKI DA ZAKU BI DON KARYA ASIRI KO SIHIRI.

 Yadda za a karya asiri ko sihiri cikin sauki ko rashin Lafiyar da aka kasa gane kanta Insha Allah

Wannan hadi ba iya maganin asiri ko sammu kwai yake ba yana maganin cutar da aka kasa gane ta kwata kwata insha Allah.


Sau da dama a wannan zamani hassada da ƙyashi sunyi yawa a wurin jama’a, yayin da zaka ga mutum gidan ku ɗaya dashi amma kuma yana yi maka baƙin ciki akan dan wani abu da kake dashi ko kuma wani matsayi daka taka a wannan duniya.

Wanda hakan yake janyowa kaga mutum yay wa dan uwansa Musulmi Jifa Ko asiri da wata cuta kokuma wani yanayin da mutum zai kasa gane kansa a wannan duniya.

To ga masu irin wannan matsala insha Allahu idan kukayi amfani da wannan haɗin maganin insha Allah za’a ga waraka cikin yan kwanaki

Abubuwan da za a nema sun hada da:

1. Qaiqayi Koma Kan Masheƙiya,

2. Farfatsin Qira,

3. Ruwa.


Da farko shi wannan ƙaiƙayi koma kan Masheƙiya zaku iya samun sa wurin masu saida magani ko kuma ƴan ganye.


Haka nan Farfatsin ƙira shima idan kuka je Maƙera, gurin masu yin fatanya, garma, Gatari dadai sauransu kuka tambaye su zasu baku shi.

Bayan kun samu waɗannan abubuwa biyu saiku dakesu sosai a turmi sosai.

Sai a samu ruwa mai tsafta a zuba a ciki ya juƙu sosai, sai a dinga sha ana kuma wanka dashi.

Nasha din idan ka debona Kofi za ka sha ka karanta Qula'uzai a ciki sannan sai asha.

Insha Allahu cikin kwanaki uku zaka shamamaki..

Comments