Main menu

Pages

KO KINSAN ZA'AFARAN DA KUMA AMFANIN DA YAKE A JIKIN MACE

 



Amfanin Za'afaran Guda Sha shida (16) wajen inganta Lafiyar jiki Maza da Mata

 Shi Za'afaran wata ciyawa ce ko kuma tsiro mai ɗauke da launi mai abin sha'awa, galibi jar ciyawa ce ko yaluwa. Da akwai man Za'afran, da akwai turarensa kuma ana samun ciyawar tasa ma.

Ana amfani da shi wajen sinadarin girki kuma yana maganin cututtuka da dama yana kuma kyautata lafiya. 



An fara noman Za'afaran ne a wajejen Greece. Sannan a kayi Safararsa zuwa Yammacin Amurka da kuma ƙasashenmu na Afrika.



Za'afaran yana maganin cututtuka kamar:

 - Zubewar Gashi.

Shafa Man Za'afaran a fatar kai yana maganin sanƙo. Haɗa Za'afaran da madara a shafa a kai yana maganin zubewar gashi kuma yana ƙara yawan gashi. 



 - Gyaran Fuska

 Haɗa Za'afaran da madara a shafa a fuska a hankali amma a kaucewa ido. A bar shi tsawon minti goma sha biyar sannan a wanke da ruwa yana sa fuska tayi kyau da sheƙi. Ana yin wannan haɗin sau ɗaya a sati.



 - Matsalolin fata.

A jiƙa ciyawar Za'afaran a ruwa tsawon awa biyu zuwa uku. Sai a shafe fatar jiki da shi. Yana bada fata mai laushi da taushi. Ana yin haka sau biyu zuwa uku a sati.



  - Maganin ƙuraje.

A haɗa Za'afaran da Ray'han a kirɓa a shafa a kan fata sai a wanke bayan minti goma. Wannan haɗin yana maganin ƙuraje, ƙyasbi, makero da tabo da kuma sauran cututtukan fata.



- Ƙwayoyin Cuta.

Zuba ko fesa Za'afaran a waje yana maganin ƙwayoyin cututtuka da ba'a iya ganinsu kuma yana kyautata lafiya.


- Kyautata Bugun Zuciya.

Za'afaran yana da sinadarin potassium wanda ke kyautata bugawar zuciya da kuma bata damar yin aikinta yadda ya kamata.



 - Zagayawar jini.

Za'afaran yana da sinadarai irinsu coper, potassaium, calcium, manganese, iron, magnesium, da zinc da  kuma selenium. Wasu daga cikin waɗannan sinadarai suna taimakawa wajen daidaita yanayin jini a jikin mutum.



- Rigakafin Cutar Kansa (cancer).

Za'afaran yana ɗauke da wasu ƙananan sinadarai kamar zea-xanthin da lycopene waɗanda ke kare jikin mutum daga kamuwa da cutar Kansa wato Daji.



  - Sauƙaƙa Narkewar Abinci.

Za'afaran yana da muhimmanci wajen sauƙaƙe narkewar abinci a jikin mutum saboda sinadarin anti-cinvulsant da sauran sinadarai dake cikinsa.



 - Ciwon Haƙori.

Shafa Za'afaran haɗe da Zuma yana taimakawa wajen maganin cututtukan dasashi da haƙori.



- Cututtukan Cikin Baki.

Idan aka haɗa Za'afaran da Zuma da Graceline ana shafawa a cikin baki yana maganin ƙuraje da sauran cututtukan da kan iya samuwa a cikin baki.



- Gyaran leɓe.

Za'afaran yana cikin tsirrai kadan waɗanda ke samar da sinadarin vitamin B2 mai yawa. Amfani da shi yana gyara laɓɓa da kuma kyautata haɗiyar abinci daga baki zuwa maƙogwaro.



- Maganin Sanyi da Tari.

Idan aka haɗa Za'afaran 1grm da ruwa 1 Litter aka sha yana maganin Sanyi da kuma Tari.



- Jini lokacin Al'ada.

Za'afaran yana da kyau wajen daidaita zuwan jini yayin al'ada.



 - Maganin Maza.

Amfani da Za'afaran yana taimakawa mazaje su dawo da ƙarfinsu. Hatta tsofaffi yana ba su kuzari sosai.

   


- Maganin Aljanu da Sihiri. 

Haɗa Za'afran da Jan Almiski da Ambar, a dinga shafawa a fata, yana maganin cututtukan Aljanu kuma yana taimakawa wajen ɓata sihiri da ke jikin mutum. 



     Amma a kula 

☆Yin amfani da Za'afaran ba bisa ƙa'ida ba zai iya sawa mutum:- 

Mura, Ciwon Kai da kuma Ɗaukewar Miyau a baki.


 ★ Masana harkar lafiya ba suyi bayanin illar Za'afaran ga mace mai ciki ba, sun ma dai ce yana taimaka mata.


 

Comments