Main menu

Pages

ABUBUWAN DAKE HADDASA MOUTH ULCER (GYAMBO KO KURAJEN BAKI)

 



Abinda ke Kawo mouth ulcers Kurajen baki da yadda za a Magance shi

Mouth ulcer wanda a Hausance za mu iya fassarawa da gyambon baki kamar yanda ake gani a hoton dake sama.Yana somawa ne da dan karamin Kurji mai zafin gaske wanda yakan tsiro a ko wane sashe daga cikin baki wanda daga nan sai ya ci gaba da lailayi yana kara fadi da girma ta yanda ko magana da cin abinci zai gagari mutum.





A wasu lokutan kurajene zasu fito da yawa a cikin baki fiye da uku ko 4 wanda idan ka ta6o da harshenka to zaka jisu a inda suka tsira.

Wasu kan yi wadannan kurajen ne kawai a sanda suka hadu da wata jinya.





Sai dai kuma idan mutum ya kasance yana yawan fama da wadannan kurajen a cikin baki to akwai bukatar bincike (diagnosis) dan a gano ainihin musababbin faruwar haka. Domin akwai abubuwa da dama dake janyo gyambo irin wannan daga cikinsu akwai wadanda gadon su ake yi daga iyaye ko kakanni.




2. Akwai herpes simplex Virus (HSV). Da kwayar cuta ta Virus ke haddasawa duk da yake sun fi bayyana a saman le66an baki (lips).Sai dai idan cutar taiyi yawa to takan iya komawa a ciki ta canza siga ta rinka haifarda gyambo irin wannan.




3. Stomatities - Wata cuta ce dakan iya  shafuwar ciki da hanji,tana haifarda kumburin ciki ko tsuwar hanji da sauyawar bayan gari ya koma daukeda majina mai yauqi da wari ,ga tsananin kasala da rama da zazza6i sai wadannan kurajen daka iya fitowa a cikin baki.


4. Stress - Damuwa tana iya haifar da wannan kurjin a cikin baki.


5. Autoimmune disoders


6. Acidic food- kamar su timatir da abu mai tsami.


7. Irritable bowel syndrom


8. Chron's disease


9. Celiac disease


10. Vitamin deficiency


11. H.I.V


12.Weak Immunity.


13. Hormones


14. Tooth paste containnig Sodium lauryl sulfate.


Yadda za a Magance wannan matsala shine za'a iya Amfani da

Man Kwakwa, Man Kanunfari, Ruwan Gishiri, Poppy seeds, Kankara, Kicocite roots, holy bassel leaves.



A guji cin abinci mai yawan gishiri da tsami da zafi da kuma yawan zaqi.


A Yawaita  tsafta da yin aswaki a kai a kai.


A Yawaita cin abinci mai vitamins da amfani da ganyayyaki.


A guji yin brush da maklin dake da sinadiran sodium lauryl sulfate.

Allah Ya sa a dace Ameen.

Comments