Main menu

Pages

SHEIKH IDRIS YA LISSAFO LAIFUKA 100 NA 'YAN FILM DA SUKE HARAM

 Laifuffukan 'yan film guda 100 da Sheikh Idris ya lissafo da suke Haramun ne a Musulunci

Fitaccen marubuci Datti Assalafy ne ya wallafa wannan rubutu a shafinsa inda ya fadi cewa babban shehin malamin ya lissafa laifuffukan yan fim wanda suke aikatawa, fim sun hada tun daga na kannywood har zuwa india fim malam yace ba yan kannywood ba a fahimmci kalmar ga abinda ya wallafa.
“Babban Malamin Musulunci dodon marassa gaskiya da ‘yan bidi’ah Ash-sheikh Dr Idris Abdul-Aziz Bauchi ya taro fada da dillalen shaidan wakilan yahudawa masu bata tarbiyya wato ‘yan Fim a cewar sa.
yanzu Malam ya fara da zayyano abubuwa guda dari (100) na haram wanda ‘yan Hausa fim suke aikatawa


Khudubar juma’a da Malam ya gabatar jiya, yayi magana akan abubuwa 24 cikin 100 na haram da ‘yan fim suke aikatawa, gasu kamar haka:

1. Rashin Jin kunya (haramune)

2. Karya a maganganunsu

3. Kadaita da matan da ba muharramansu ba

4. Haduwan mata da Maza

5. Rawa da waka

6. Waka

7 Kida

8. Shiga wanda ya sabawa addini

9. Baiyana al’aura

10. Fikm Yana jawo saki tsakanin ma’aurata

11. Yin ado badon miji ba

12. Tafiye-tafiye ba da muharrami ba

13. Sabawa iyaye

14. Zagin iyayen juna

15. Kalmomin batsa

16. Bayyana barna a fili

17. Tayarda sha’awa

18. Suna sawa ayi Zina

19. Suna sawa ayi fyade

20. Koyar da sata

21. Gulma

22. Annamimanci

23. Basaja

24. Hassada


Sauran abubuwa na haramci 75 da ‘yan fim suke aikatawa suna tafe Insha Allah, na rantse da Girman Allah ‘yan fim sun taro fadan da ba zasu iya ba, Malam zai yi nasara a kansu


Ban taba ganin wanda yayi fada da Malam Idris Abdul-Aziz Bauchi ya kai labari ba, domin Wallahi Malam Idris akan gaskiya yake, shiyasa Allah Ya ke taimakonsa akan mabarnata da sauran mutanen banza, zagi da kamu da barazanan kisa baya tasiri akansa.
To Allah Ya kyauta Ya shiryar damu. Amma fa qa'idar wa'azi a Musulunci ba a kama sunan Wani, ko wata Kungiya, ko wasu Taron Mutane. To Allah Ya shiryar damu mu duka, da 'yan film din, da malaman damu masu ji da Kuma saurare.

Comments