Main menu

Pages

AMFANIN SANAMAKIY GUDA SHA TAKWAS GA LAFIYAR DAN ADAM

 



Amfanin SanaMakiy -السنامكي da yadda za a sarrafata har guda Sha takwas

Manzon Allah ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ya ce "Da za a samu abin da zai yi maganin mutuwa to da Sana(makiy) ce.


SanaMakiy wata ciyawa ce koriya mai dogon tarihi kuma tana da rijista a ofishin harhaɗa Magunguna na Manzon Allah .ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻲ ﻭﺳﻠﻢ

ﻗﺎﻝ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ

ﻟﻮﻛﺎﻥ ﻓﻲ ﺷﻲﺀ ﺷﻔﺎﺀ ﻣﻦ ﺍﻟﻤﻮﺕ ﻟﻜﺎﻥ ﻓﻲ ﺍﻟﺴﻨﺎ.

Manzon Allah ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ Ya ce "Da za a samu wani abu wanda maganin mutuwa yake a cikinsa to da a cikin Sana(makiy) za a samu"


Likitoci Larabawa su ne suka fara amfani da Sana Makiy a matsayi magani tun shekaru ɗari tara bayan aiko Annabi Isa ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺴﻼﻡ


Haka ma mutanen Europe sun daɗe suna amfani da ita ta fuskar magani.


        

Ga jerin Amfanin SanaMakiy

1. GYARAN FATA. (oil) mai wanda yake jikin ganyen Sana Makiy yana ɗauke da sinadaran da ke gyara fata da kuma maganin cututtukanta. Kamar ƙuraje da Makero da dai sauransu. Tana kuma maganin ciwo ko ƙonewa.


Sai a haɗa garin Sana Makiy da garin Habbatussauda da Farar wuta, a kwaɓa da Man kaɗanya a dinga shafawa.




2- HASKEN HAƘORA. Goge haƙori da ciyawar Sana Makiy na ƙara masa haske da sheƙi. Ana kuma iya zuba garin Sana Makiy a cikin totuwar Ayaba a Haɗa da ganyen Na'ana'a a goge haƙora don ƙara musu haske da sheƙi.




3- ƘARA YAWAN GASHI DA SA SHI BAƘI DA HANA SHI KARYEWA.

Ana iya kwaɓa Sana Makiy a cikin Man Kwa-kwa domin ƙara yawan gashi da kyawunsa.




4- RAGE ƘIBA KO TEƁA. Shan rabin cokali na garin Sana Makiy a kullum yana saurin rage ƙiba da tumbi.



5- SANA MAKIY TANA MAGANIN WASU-WASI. wanda ya takurawa mutum. Ana haɗa ta da Na'ana'a da Ray'han, a dafa a zuba zuma ana sha kullum cokali ɗaya.



6- FITAR DA GUBA Tana fitar da gubar da mutum ya ci ko ya sha a cikinsa.



7- NARKAR DA BAHAYA Tana taimakawa wajen yin bayan gida ga wanda ya kasa ko yake ba shi wahala.



8- MAGANIN BASIR Sana Makiy tana maganin Basir sosai da sosai.



9- ƘARANCIN JINI Tana Maganin ƙarancin jini a jikin mutum.



10- GYARA MAFITSARA Tana tsaftace hanyoyin fitsari kuma tana taimakawa wajen yin sa cikin sauƙi.



11- ƘARFAFA ZUCIYA Tana ƙarfafa zuciya kuma tana taimakawa mata wajen yin aiki.



12- MAGANIN SHAIƊANU Tana Maganin Aljanu idan an haɗa ta da zuma ana sha.



13- CIWON SUGA Tana maganin ciwon suga. A haɗa Sana Makiy da ɓawon kwakwa a jiƙa a ruwa. Sai a dinga sha.



14- KAWAR DA MANTUWA Yawan mantuwa. Sai a yi shayi da Sana Makiy da garin Ray'han a zuba zuma.



15- CIWON CIKI A gauraya Sana Makiy da garin Rawaya, ya zamto yawansu duka ɗaya ne, Sai a jiƙa a dinga sha.



16- MAGANIN TSUTSAR CIKI Shan garin SanaMakiy yana maganin Tsutsar ciki.


17- TANA MAGANIN MAJINA. Tana maganin Farfadiya.


18- SANA MAKIY na maganin Ciwon jiki idan ana haɗa ta da ruwan ɗumi.



        AMMA A KULA !!!

Duk da amfanin da SanaMakiy take da shi, yin amfani da ita ba bisa tsari ba yana iya cutar da mutum.


1- Mai ciki ƙasa da wata huɗu kada ta sha Sana Makiy.


2- Kada a baiwa yaro ɗan ƙasa da shekara shida.


3- Shan Sana Makiy da yawa zai sa mutum gudawa.


4- Idan mutum ya fara shan SanaMakiy fitsarinsa yana canja kala amma daga baya yana dawowa daidai.


5- Kada mutum ya yawaita amfani da SanaMakiy kowanne lokaci.

Comments