Main menu

Pages

AMFANIN GANYEN AYABA GUDA TAKWAS GA LAFIYAR JIKI

 Amfanin yin shayin Ganyen Ayaba guda takwas da cutukan da yake karewa

Mutane da yawa a duniya suna son ayaba a matsayin ya’yan itace kuma suna jin daɗin cin ayaba sosai.


Ba za’a iya watsi da ganyen ayaba saboda irin tasirin shi kan lafiyar jiki domin yana da abubuwa da yawa wadanda suke da amfani ga jikin dan adam.


Don haka da yawa mutane sun yi watsi da ganyen ayaba saboda ba su san abin da yake yiwa tsarin ɗan adam ba. Ayaba mai zaki ne kawai muke ci kuma bama kallon yadda ganyen yake.
 Amfanin Ganyen Ayaba guda takwas

1. Tana hana ciwon daji girma a jiki.

2. Ganyen ayaba in anyi shayin sa yana taimakawa wajen cire guba daga jiki.


3. Za’a iya amfani da ganyen ayaba don magance ciwon makogwaro da mura.


4. Ana iya tafasa ganyen ayaba a sha domin kawar da guba daga jiki. Don haka ana amfani da shi azaman shayi mai wanke jiki.


5. Tafasasshan ganyen ayaba na taimakawa wajen yakar kananan kwayoyin cuta masu cutarwa a jiki


6. Yana kuma taimakawa garkuwar jiki wajen yakar kwayoyin cuta da cututtuka kamar cututtukan zuciya, ciwon koda da matsalolin hanta.


7. Har ila yau shayin ganyen ayaba yana wanke zuciya, koda da hanta, ya zame masu rigakafi daga kamuwa da wata cuta


8. Suna taimakawa wajen magance tari idan ana shan shayin ganyen ayaba. A sauƙaƙe a debo ganyen ayaba, a wanke a dafa da ruwa mai tsafta, a tace a sha

Comments