Main menu

Pages

YADDA ZA A MAGANCE ZAZZABIN TYPHOID DA MALARIA CIKIN SAUKI

 


Yadda za a hada ingantaccen Maganin Typhoid da Malaria Insha Allah

Zazzabin Typhoid da maleria wasu sha hararrun ta gwayen cututtuka ne da suka dade suna addabar mutane, 

Cututtukan basu da sauki idan suka kama Dan Adam, Ga Mai fama da cutar yakan rasa inda zai saka kansa har yaji tamkar zai bar duniya sabo da tsabar zafin Zazzabin,
Idan  cutar  yayi tsanani a jikin mutum tana iya fatattaka masa hanjin cikin sa wanda zai haddasa mutum ya rasa ransa gaba daya,Alamomin Cutar Sune:

1-Yawan jin kasala ko ciwon jiki,

2-Tashin zuciya,

3-Rashin Jin dandano a baki,

4-Yawan Jin jiri,

5-Canzawar fitsari ya koma wani irin kala,

6-Rashin son cin abinci,

7-Rashin Jin karfi a jiki,

8-Ciwon kai mai tsanani,

9-Yawan amai da dai sauransu,Abubuwan da za a nema don hada maganin

1- Ganyan Rai dore, dunkulen hannu biyu

2- Ganyen Na'a Na'a, karamin kofi

3- Garin tafarnuwa. Babban  cokali 2

4- Garin habbatussaudat. Babban cokali 10

5- Ciyawar Lemon Grass.  dunkulen hannu daya

6- Zobo rodo. Kamar karamin kofi 

7- Bawon Abarba. Kamar cikin karamin kwano 

8- Lemon tsami. Guda 10

9- Ruwa.  4Litters.
Yadda Ake Hada wannan Magani

Za'a yayyanka lemon tasamin sannan sai azuba duk wadancan abubuwan da muka lissafo har da ruwan lita hudu sannnan a Dora akan wuta a tafasa shi sosai bayan ya tafasa sai a sauke.
Yadda za a Sha maganin

Ana Shan karamin kofi daya sau uku a rana safe da rana da kuma dare,


Wannan mujarrabun ne domin kuwa bansan wani maganin da yake kawar da zazzabi farat daya kamar wannan hadin maganin ba cikin yaddar Allah.

Taifot koda ya kai tsawon shekaru a jikin mutum inshaAllahu sai ya warke,

Comments