Main menu

Pages

AMFANIN LEMUN TSAMI WAJEN GYARAN FUSKA, GASHI, DA KUMA FUSKA

 Amfanin Lemun tsami ta fuskar gyaran Fata, Fuska da Kuma gashi

Dukanmu mukan yi amfani da lemo sau da yawa, amma yawancin mu ba ma san ainihin amfanin sa ba musanman ga mata. Ana iya amfani da lemon tsami a kicin, amma ba iya nan amfanin sa ke tsayawa ba. 
Kamar yadda wataƙila kun riga kun sani, lemun tsami yana ɗauke da sinadaran bitamin B da C, da calcium, potassium, magnesium da phosphorus. Wanda suke da kyau ga lafiyar mu.

Lemun tsami na iya inganta jiki, magancewa da hana kamuwa da cuta, yana ƙarfafa tsarin garkuwar jikin mu har ma da rage yawan nauyi. Ana iya amfani da su ta hanyoyi daban-daban, amma a cikin rubutun yau, zan nuna muku yadda ake amfani da su don magance wasu matsalolin.


Anan akwai hanyoyi guda 3 da ake amfani da Lemon tsami wanda yakamata mace ta sani kamar haka.

Yana Sanya Fata tayi kyau tayi taushi. 

Shafa ruwan Lemon Tsami yayin kwanciyar bacci kansa ya fatar jikin ki tayi kyalli da laushi, da kuma kashe wasu kwayoyin cututtukan da ke a jikin fata.

Yana Haskaka Gashi yayi ta sheki

Kusamu ruwan Lemon tsami ku shafa a gashin kanku saiki barshi ya bushe zuwa wani dan lokaci sai a wanke da ruwan ɗumi, zai sanya gashin kanku kyalli kana yayi baki da tsawo kuma ya kashe muku ƙaiƙayin gashin kai.

Yana kawar da Tabon Fuska

 Sanya ruwan Lemon Tsami akan tabo dake jiki kan kawar da duk wani tabo dake jikin ki, kawai a samu auduga sai a dangwali ruwan Lemon Tsami a goga a inda tabon yake. Allah yasa mudace.

Comments