Main menu

Pages

FIRAN HADIZA GABON DA FATI WASHA AKAN YADDA TA FITO A LABARINA

 Yadda Firan Hadiza Gabon ta kasance da Fati Washa akan shiga Shirin Labarina

A wata hira da Jarumar masana’antar kannywood Hadiza Gabon ta tattauna da jaruma Fati washa

a shirin GABON’s ROOM, jaruma Washa ta bayyana ita aka fara nema ta taka rawar SUMAYYA a shirin LABARINA tun ashekarar 2016, amma Mawaki kuma Producer Nazifi Asnanic ya nuna bayaso shi akwai wacce yafi gamsuwa da ita.

Mai shirin tana cewar yanzu dai gashi kina cikin Labarina Dumu dumu yah akayi haka

Hadiza Gabon: miyasa tun farko baki shiga labarina ba sai yanzu?


Fati washa : tun farko abinda yasa ban shiga labarina ba saboda lokacin da aka zo an dan samu problems da clashing na Irin haka haka wasu nada ra’ayin wadanda suke so a saka a fim din irin su Nazifi Asnanic wanda suke da ra'ayin wanda za’a saka.


Hadiza Gabon: ma’ana shi yace baya son a sanya fatima sai dai wata?

Fati washa: Eh, Gaskiya haka labarina ya zo min.


Hadiza Gabon: to amma nasan yadda kuke da Nafisa kawaye kuke da ita bai kawo muku sabani ko kuma matsala tsakaninku ba.?
Fati washa : Eh Gaskiya ni bai kawo muna matsala ba, saboda abu ne wanda bansan yadda akayi daga furodusa din ba har darakta ba miye tsakaninsu ba kuma banso inji ba kawai dai ni kirana akayi ita kanta tasan haka..


Ga bidiyon hirar nan zaku iya sauraren domin kuji daga bakinta.
Comments