Main menu

Pages

ABUBUWAN DA MAI CIKI ZATA HADA DON SAMUN SAUKIN LAULAYI




Kina fama da Matsanancin Laulayi yayin da kike da ciki, to ga abin da Zaki hada don samun sauki.

Laulayin ciki abu ne wanda yake zuwa bisa yanayin halittar da Allah ya yiwa Mace.

Domin akwai bambanci a tsakanin su kansu matan, wata matar tafi wata shan wahala a lokacin laulayi.




Ga wasu magunguna nan a nema a hada, Insha Allah za a dace:

(1) Ganyen Na'a-Na'a (Fresh ko busasshe mai kyau).

(2) Lemon tsami.

(3) Zuma mai kyau.

(4) Citta da Kanumfari.


A dafa ganyen Na'a-Na'a kamar cikin tafin hannu 2 a cikin ruwa kofi 3, a zuba citta da kanumfari daidai misali a dafa su tare.

Idan an sauke, an tace ruwan sai a zuba zuma gwargwadon yadda ake so, sannan a yanka lemon tsami guda biyu (me ulcer Rabi), a matse a cikin ruwan da aka dafa din sannan asa a flacks ana sha kadan kadan wuni daya a shanye za a samu sauki Insha Allah





Amfanin da Wannan hadin zai yi

Mai Juna biyun za ta samu qarfin jiki, za ta dena yawan zubar da yawu (Miyau) da hararwa (amai) kuma jaririn dake cikinta zai samu kaifin basira da kwakwalwa Insha Allah.



- Allah ya sauki dukkan masu juna biyun Musulmai Lafiya. Wadanda aka haifa kuma Allah ya raya mana su.


- Marasa yara Allah ya basu masu albarka.

 

- Mata masu planning kafin aure ku kiyaye akwai nadama sosai.

Comments