Main menu

Pages

HANYA BIYU DA ZAKI HADA DILKA CIKIN SAUKI JIKINKI YAYI KYAU




Yadda zakiyi hadin gyaran jiki na dilka cikin sauki a wannan lokacin na Sanyi.

1. Man Zaitun

2. Lalle

3. Kur-kur

4. Madarar ruwa (peak)


Za ku hade wadannan kayan hadin guri guda sai ku kwaba su ku shafe jikinku da fuskar ku, za ku yi wannan hadin kafin ku shiga wanka idan ya bushe a jikin ku sai ku murje sannan sai ku shiga wanka,

wannan hadin ya na sa jiki yayi kyau da sheki insha Allahu.





Za ku iyayin wannan ma wanda ake hada:

1. Kur-kur

2. Dilka

3. Zuma kwai

4. Lemon tsami

Za ku hade su a guri guda ku samu ruwa ku kwaba kamar yadda ake kwaba lalle, amma ya fi kwabin lallen ruwa, sai ku shafe fuskanku, idan kuma har da jiki kuke so, sai ku shafa har da jiki bayan awa daya sai ku shiga wanka za ku ga yadda jikinku zai goge. Das da izinin Allah.

Comments