Main menu

Pages

YANDA ZAKI HADA SHAYIN RAGE KIBA CIKIN SAUKI A GIDA

 
Yanda Ake Hada shayin rage kiba a gida Kuma cikin sauki

1. Lemon grass

2. Ginger

3. Tafarnuwa

4. Cardamom

5. Cinnamon

7. Kanumfari

8. Garin zogale

9. Green tea 

10. Zuma

11. Lemon

12. Apple cider venegarYanda za a Hada

Za a samu duka kayan dana ambata asama duka a wanke a adafasu( lemon grass, ginger,tafarnuwa, cardamon,cinnamon, kanumfari,garin zogale) a dafasu su dahu.

A wanke lemon a yanka a ciki ko a matse ruwan in an sauke.

Sannan in a misali karamin kofin tea ne sai ki zuba tea spoon na apple cider venegar, sai ki kwankwade kina shanyewa da zafi zafinsa zufa zai fara keto miki sai ki dan yi tsalle tsalle ko ki shiga aikin gida kina yi cikin sauri ki yi ta zuba. Haka nan ki sha shi da daddare bayan kin gama komai zaki kwanta. In kin ji yunwa sai dai kisha fruits ko vegetables amma ban da carbohydrate.

Idan kuma kina da ulcer ko jikinki baya son lemon to ba sai kin sanya ba, sai ki nemi irin green tea mai haďe da lemon. Sannan zogale in baki samu ready made ba to ki sa a samo miki danyen sai ki shanya shi a inuwa kada ki shanya shi a rana nan da nan zai bushe.

Comments