Main menu

Pages

NAU'IKAN ABINCI BIYAR DA AKA HARAMTAWA MAI CIKI CIN SU

 



Nau'kan abincin da aka haramtawa Mai ciki cinsu

Masana harkar kiwon lafiya sun haramtawa mace mai juna biyu cin wasu nau’ikan abinci wanda a ganinsu zai iya kawo barazana ga lafiyar mai cikin ko ‘dan da ta ke dauke da shi.




Daga cikin nau'kan abincin sun hada da;

1. Ganyen da ba a wanke ba duk da cewa ganye na da amfani musamman ma ga mai ciki, amma dole masu juna-biyun su kiyayi cin ganye irin su latas da alaiyyahu da ba a wanke da kyau ba.





2. Giya Ko ya mai ciki ta sha giya yana iya yi mata mugun illa. Haka nan kuma ana so masu shayarwa su guji giya domin tana iya kawo babbar matsala a jikin su.





3. Sinadarin caffeine Haka kuma ya zama dole mai ciki ta kiyayi daukar abubuwan da ke dauke da caffeine. Sinadarin na iya jawo bari, ko haihuwar bakwaini ko a fito da yaro ba lafiya.





4. Madarar da ba a dafa ba Masana sun bayyana cewa dole mai ciki ta kiyayi shan danyan nono na madara da ba a tafasa ba. Madara na dauke da listeria wanda zai iya yi wa mai juna biyu illa.




5. Kifi da nama da kwai Masu ilmin kiwon lafiya sun haramtawa masu ciki cin ‘danyen kwai da ba a dafa ko aka soya ba. Haka kuma a guji kifin (na gwangwani ko wanda aka gasa ko wanda ya sha wata cuta a ruwa) sannan kuma guji cin naman da bai nuna ba

Allah ya raba lfy

Comments