Main menu

Pages

YANDA ZA A MAGANCE GAUTSI DA KAUSHIN FATA CIKIN SAUKI

 Hanyoyi har guda takwas da zaku bi don magance Kaushin Fata da Gautsinta

Akwai abubuwa da dama da suka kamata a yi domin rage kaushin kafa ko rabuwa da shi baki daya. Kaushin kafa yana yawan fito wa mutum ne a lokacin sanyi sakamakon abubuwa kamar; yawan shekaru da rashin cin abinci mai gina jiki da kuma jinsi. Akwai nau’o’in mai da dama da ake sayar dasu domin magance matsalolin kaushin fata amma yawancinsu suna da tsada. 
Domin bin hanya mafi sauki wajen magance wadannan matsaloli na fata sai ku karanta abubuwan da na lissafo muku.- A rika diga man zaitun a cikin man shafawa. Yin hakan na sanya fata laushi kuma yana rage kaushin fata.- Lemun tsami da sukari suna taimakawa wajen fitar da fatar da ke da gautsi a jiki sannan suna sanya fata haske. A samu sukari kamar cokali daya sannan a matse ruwan lemun tsami a ciki sai a rika shafawa a fuska a bari na tsawon minti uku sannan a wanke.
- Za a iya kwaba fiya sannan a shafa a jiki a bari na tsawon minti 15 sannan a wanke kafin a shiga wanka a kullum. Ko kuma a hada jus din fiya a rika sha domin magance kaushin fatar daga jiki.
- A rika amfani da man kwakwa a fatar jiki. A dora man kwakwa a wuta ya dan yi dumi sannan a shafer fatar jiki kaf da shi na tsawon minti 30 kafin a shiga wanka a kwanta. A rika yin haka kullum.
- Shan madara kofi daya kafin a kwanta barci a kullum na taimaka wa fata sosai.
- A rika shafa man kadanya a jiki bayan an yi wanka da dare kafin a kwanta barci. Sai a mulke jikin gaba daya da man kadanya domin samun fata mai laushi mai sheki.
- A samu ayaba da nono ko kindirmo a kwaba a waje daya sai a shafa a fuska ko fata na tsawon minti 20 sannan a wanke da ruwan dumi.
- A shafa zuma a fatar jiki baki daya sannan a bar ta na tsawon minti biyar zuwa 10 kafin a shiga wanka a kullum.
A yi amfani da daya daga cikin abubuwan da na lissafo. Kada a hada duka a jiki, amfani da abubuwa da yawa a fata yana haifar da kuraje a fata.

Comments