Main menu

Pages

YANDA WATA MATA TA KASHE KANTA SABODA MIJINTA ZAI KARO AURE

 Wata Mata ta kashe kanta saboda Mijinta zai karo Aure

Ana zargin cewa wata mata mai suna Yetunde Folorunsho ta kashe kanta ta hanyar shan gubar maganin ƙwari domin ta hana mijin ta mai suna Dare Araoje ƙara aure. Lamarin ya faru a Ilorin jihar Kwara.
Dailytrust ta wallafa cewa wannan lamari dai ya faru ne a garin Ilorin na jihar kwara inda matar wacce take da ƴaƴa guda biyu tare da mijin ta suke zaune.
Mai magana da yawun hukumar ƴan sanda na jihar kwara Ajayi Okasanmi ya shaidawa manema labarai cewa binciken da suka gudanar akan gawar matar ya tabbatar da cewa lallai ta sha maganin ƙwarin nan ne da ake kira da ‘sniper’ wanda shine yayi ajalin nata.
Matar, wacce tayi digirin ta a ɓangaren nazarin yaruka, wacce kuma ƴar asalin jihar Osun ce ta mutu ne a lokacin da ake kan hanyar kaita asibitin gwamanti dake garin Ilorin. Mutuwar matar ta kawo ruɗani a tsakanin dangogin biyu.
Sai dai kuma lamarin ya kawo ruɗani a tsakanin dangin matar da kuma dangin mijin nata, inda danginta ke zargin cewa mahaifiyar mijin ce ta sanya mata gubar a abinci sabili da saɓanin addini da suka samu.
Majiyar tamu ta ƙara da cewar a can baya Matar ta kasance tana bin addinin Kiristanci, amma daga bisani sai ta karɓi Musulunci, matakin da kwata-kwata bai yima ‘yan uwanta daɗi ba.
Ƴan uwanta sun tsayu akan cewa lallai fa su sun tabbatar da cewa matar ba zata iya kashe kanta ba, illa iyaka dai kawai an kashe ta ne.

Sai dai kuma majiyar tamu ta bayyana cewa mazauna yankin da lamarin ya faru sun shaida musu cewa fa lallai matar ta kashe kanta ne ta hanyar shan guba saboda saɓanin da suka samu da mijin ta kan batun ƙara aure da yayi.

Matar ta tabbatar da haka kafin mutuwar ta

Wani ɗan uwan mijin mai suna Lagbe Araoje ya shaida ma ‘yan jarida cewa matar ta ɗan samu saɓani da mijin amma kuma an sasanta su, tunda har waya ma mijin ya siya mata bayan nan.
“Bayan nan sai ta shiga gida. Can ba da daɗewa ba sai ga mijin mata ya fito yana kuka ya na neman jama’a su kawo mishi ɗauki matar shi na ta amai. Akan hanyar mu ta zuwa asibiti ne ta roƙi mijin akan ya yafe mata domin kuwa ta sha maganin ƙwarin da ake cema ‘sniper’ .” inji shi.
Mai kyamis ɗin da ya siyar ma da matar maganin ya tabbatar ma da manema labarai cewa lallai gurin shi ta sayi maganin, sai dai bai yi zargin cewa zuwa zata yi ta sha ba.

Comments