Main menu

Pages

AMFANI LALLE TARA DA YA KAMATA KU SANI WAJEN GYARAN FATA

 
Amfanin Lalle guda Tara da ya kamata kowa ya sani wajen inganta fatar jiki

Ga kadan daga cikin amfanin lalle da muka zakulo muku:

CIWON KAFA: Yin lalle na rage ciwon kafa. A kwaba lalle da ruwa ya yi kauri, a shafa wa kafar na tsayon lokacin da ake bukata sannan a wanke. Yin haka na rage radadi da zugin da ke damun mutun a kafarsa.

DATTIN CIKI: Shan ruwan lalle na wanke dattin dake ciki. Idan aka jiga lalle da ruwa aka tace, sai a sha ruwan daidai gwargwado. Yin hakan na wanke dattin ciki.

GYARAN FATA: Ana amfani da lalle wajen gyara fatar jiki da kawar da datti da kuma sanya fata haske mai kyau. Domin haka, sai a zuba lalle da ruwa a rika wanka da ruwa lallen akalla so daya a rana.

FATAR FUSKA: Lalle na sa fuska ta yi laushi da haske. Bayan an kwaba lallen da kauri a rika goga fuskar ta ita. Bayan minti 20 zuwa 30 sai a wanke fuskar da ruwa. Za a iya yi sau daya zuwa uku a rana.

KURAJEN FUSKA: Ga masu fama da kurajen ‘pimples’ sai su kwaba lalle da ruwan lemon tsami ya yi kauri suka rika shafa kwabin a fuskar. Zuwa wani lokaci pimples din za su bace.

AMOSANIN KAI: Ana a wanke gashin kai da ruwan lalle domin maganin amosarin gashi. Ana yin hakan ne ta hanyar kwaba lalle a ruwa ya yi dan ruwa-ruwa sannan a jika gashin a cikin ruwan. Bayan minti 20 sai a wanke kan. Yawan yin hakan na kashe amosarin kai.

GYAMBON YATSA: Masu gyambon yatsa (dankankare) na amfani da lalle wajen neman sauki. Akan kwaba shi a sanya a wurin da ke da gyambon a yatsar don neman waraka ko busar da shi.

KWALLIYAR GASHI: Maza da mata na amfanin da shi domin kwaliya a gashin kansu da kuma gemu. Domin yin hakan, sai da a kwaba lalle da ruwa a shafa a wurin da ake bukata na ‘yan mintoci sannan a wanke.

ZAYYANA FATA: Ana kuma amfani da lalle wajen yin ado ta hanyar zayyana a fatar ji. Akan kwaba lalle ta yi kauri, sannna a lika leda mai dauke da nau’in zayyanar da za a yi a fatar, sannan a shafa lallen a sama. Daga nan sai a bar shi ya yi awanni kafin a wanke. Ana kuma iya yin zayyarar kai tsaye da kwababben lallen ba tare da sanya ledar ado ba.

Comments