Main menu

Pages

AMFANI BIYAR DA AGWALUMA KEYI GA JIKIN DAN ADAM

 



Amfani biyar da agwaluma keyi ga jikin Dan Adam

1. Agwaluma na maganin zazzabin Malaria mai naci ko wanda bai jin magani. Binciken wanda aka wallafa a kundin BMC Complementary and Alternative Medicine ya bayyana cewa wannan magani ka iya zama sabuwar karbabbiyar hanyar magance zazzabin duba da rashin nasarar da ake samu da sauran nau’ikan magunguna.




2. Agwaluma na dauke da sinadarin Vitamin C, wanda ke da matukar amfani a jikin dan adam.




3. Agwaluma na da matukar amfani ga mai dauke da juna biyu. Shan agwaluma na tsayar da amai da jiri wanda juna biyu ke haifarwa.





4. Sannan idan mutum baya so yayi kiba daya wuce misali sannan yana bukatar sinadarin gyaran idanu da zuciya toh agwaluma na taimakawa sosai wajen cimma hakan.




5. Yana kuma taimakawa wajen samun bacci cikin kwanciyar hankali. Sannan kuma yana rage ciwon gabobin jiki.


Comments