Yadda Ake Hada Sabulun Fuska, tayi kyau da sheki
・ Sabulun salo
・ Sabulun zuma
・ Zuma
・ Aloevera
・ Man zaitun
・ Kwakwa.
A samu sabulun salo ko sabulun ghana kamar girman sabulun giv guda biyu, a samu sabulun zuma guda daya idan ba a sameshi ba a sa alorvera soap, a daka sabulun ko a goga a sa ruwan ganyen alorvera cokali uku, zuma cokali uku, man zaitun cokali daya, man kwakwa cokali daya, a hada a kwaba, a dinga shafawa a fuska, bayan minti goma ko sha biyar a wanke fuskar yana saka kyan fuska tayi shaining ta yi kyau.
Sabulun wanka na bakar mace
↳ Sabulun salo ko sabulun ghana
↳ Majigi
↳ Zuma
↳ Lemon tsami
↳ Zaitun.
A hada sabulun ghana da majigi a dake a zuba zuma a matsa lemon tsami kadan a saka man zaitun cokali daya a bada a kwaba, bakar mace da bata son ta yi fari sai ta
dinga wanka da shi, zai sa tayi kyau, fatarta tayi taushi da santsi bakinta ya dinga kyalli.
Don gyaran gaba, Matsi da Karin Ni'ima
♧ farar albasa
♧ kanumfari
♧ balmo/barkono.
sai ki hade su guri daya ki dinga cin abinci da wannan hadin.
da farko ana so awa 2 ko 3 kafin ki kwanta barci ki shafa man goge baki a fuskarki musamman wuraren pimples suke da yawa, ba kowane zaki shafa ba ana so ki shafa
farin man goge baki wato (maclean) idan kika ga dama za ki iya wanke fuskar da man goge baki ya yi kamar 30, idan kin ga dama kuma zaki iya kwantawa dashi har zuwa
wayewar gari za kiyi hakan har zuwa lokacin da zaki ga
canji fuskar ki
Comments
Post a Comment